Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

  • A ranar Litinin, Bola Ahmed Tinubu ya yi rantsuwar zama sabon shugaban kasa na 16 a Najeriya
  • Sabon shugaban ya dauki wasu alkawura a jawabin da ya gabatar a karon farko bayan karbar mulki
  • Bayanan sun shafi yadda za a kawo cigaban tattalin arziki da ayyukan yi da matasa za su mora

Punch ta kawo rahoto da ya tattara muhimman bayanan da su ka fito daga bakin Bola Ahmed Tinubu:

1. Tsaro

Gwamnatin Bola Tinubu za ta yi wa tsarin tsaro garambawul tare da maida hankali a kan karin jami’an tsaro da horaswa, tanadin kayan aiki da albashinsu.

2. Tallafin man fetur

Sabon shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa tayi waje da tsarin tallafin fetur, ya ce za ayi amfani da kudin a samar da ayyukan yi, kiwon lafiya da ilmi.

Kara karanta wannan

Fetur Ya Haura N300 a Gidajen Mai Daga Jin Bola Tinubu Ya Sanar da Janye Tallafi

Bola Tinubu
Sabon Shugaban Kasa, Bola Tinubu a Eagle Square Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

3. Ayyukan yi

Bola Tinubu ya ce zai yi kokarin hada-kai da ‘yan majalisa domin bude hanyoyin kwadago da ayyukan more rayuwa domin matasa su samu ayyukan yi.

4. Kamfanoni

A yunkurin rage zaman banza, gwamnatin nan za ta goyi bayan kamfanonin gida domin a rage dogaro da kaya daga ketare kuma mutane su samu sana’a.

5. CBN da canjin kudi

Baya ga sake duba tsarin canjin kudi da aka yi, Tinubu ya na so a rage ruwan bashin banki, sannan CBN ya maida hankali wajen daidata farashin kudin waje.

6. Abokan adawa da sauransu

Sabon shugaban ya yi alkawari zai mutunta abokan gabarsa a zaben da ya yi ikirarin ya yi nasara da gaskiya, ya ce zai saurari koken duk wani mai korafi.

7. Mata da matasa

Kamar yadda ya yi alkawarin tafiya da matasa, The Cable ta ce Tinubu zai dage wajen ba su muhimmanci, sannan za a inganta abubuwan more rayuwa.

Kara karanta wannan

A Ranar Farko, Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Mai Kyau Kan Sauya Takardun Naira

Sabon Gwamnan Kano

Jim kadan bayan an rantsar da shi, an ji labari Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya fara aiki a kan kujerar Gwamna a jihar Kano.

Dr. Baffa Bichi ya zama sabon SSG, Shehu Wada Sagagi zai rike gidan Gwamnati, yayin da aka nada Dr. Faruk Kurawa a matsayin babban Sakatare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel