Tinubu: Kashim Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

Tinubu: Kashim Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

  • Kashim Shettima ya yi jawabi wajen laccar shirye-shiryen ransar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Mataimakin shugaban kasa mai jiran-gado ya ce da farko gwamnatinsu za ta ci karo da kalubale
  • Shettima ya na sa ran bayan abubuwa sun lafa, su iya gano kamun layin tattalin arzikin Najeriya

Abuja - A yunkurin ragewa mutanen kasar nan dogon buri, an ji Kashim Shettima ya na cewa gwamnatin mai gidansa za ta fara mulki ne a kan gargada.

Da yake jawabi a laccar da aka shirya domin rantsar da sabon shugaba, Channels TV ta rahoto Kashim Shettima ya na fadan abin da ya kira gaskiyar zance.

Zababben mataimakin shugaban kasar ya sha alwashi cewa Asiwaju Bola Tinubu zai dumfari aiki da zarar sun shiga ofis a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

A ina matsalolin su ke

Daga cikin abubuwan da Sanata Shettima ya fara kokawa da su akwai tsarin tallafin man fetur.

Tsohon ma’aikacin bankin ya nuna sai gwamnatin Tinubu mai jiran-gado ta dage wajen tabbatar da cewa babu wani bambancin farashin kudin ketare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da farko ba dole abubuwa su zo da sauki ba, bari in fada maku gaskiya. Tallafin man fetur ya zama ala-ka-kai a kan mu.
Ana fama da farashin kudin kasar waje iri-iri, wadannan abubuwa sun zama mana matsala, sun birkita tattalin arziki.
Akwai matakan da sabuwar gwamnati za ta dauka, amma bayan lokaci mutanen Najeriya za su yabawa kokarinmu."

A jawabinsa a babban masallacin kasa da ke Abuja, shugaban mai jiran gado ya ce ubangiji ya yi masu baiwa da suka samu mulki ba don sun fi kowa ba.

Tsohon Gwamnan na Borno ya ke cewa za su yi amfani da damar domin bautawa al’umma, ya tunawa kansa cewa ba za a dade ba za su bar gadon-mulki.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Gwamna Ya Nemi Alfarmar Karshe Kafin Buhari Ya Bar Fadar Aso Rock

Shettima ya dauki lokaci ya na yabon Tinubu, ya ce zai yi wa kowane ‘dan Najeriya adalci ba tare da fara duba ga addini, kabila ko yankin da mutum ya fito ba.

A cewarsa, lokaci ya yi da za a hada-kai domin ceto kasa daga talauci, kangi da rashin tsaro.

Lamarin Nnmadi Kanu

Labari ya zo cewa Gwaman Anambra, Farfesa Charles Soludo ya rubutawa shugaban kasa wasika kan batun Nnmadi Kanu da yake daure tun shekarar 2021.

Gwaman na jihar Anambra ya ce rashin tsaro ya addabi Kudu maso gabas saboda tsare shugaban IPOB saboda haka ya bada shawarar ya samu 'yanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel