Sabon Bincike Ya Nuna Lokacin Da Ya Fi Dacewa Namiji Ya Kwanta Da Matarsa Su Raya Sunnah

Sabon Bincike Ya Nuna Lokacin Da Ya Fi Dacewa Namiji Ya Kwanta Da Matarsa Su Raya Sunnah

  • Wasu kwararrun masu bincike a Burtaniya sun gano lokacin da ya fi dacewa mutane su kwanta da matansu na aure
  • A cewarsu bayan tashi daga gado da ƙarfe 7:00 na safe, mintuna 30 bayan haka ya fi kamata ma'aurata su ji daɗin juna
  • Binciken ya yi bayani sosai kan yadda ya kamata mutane su riƙa tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum

Wani sabon bincike da aka gudanar a Burtaniya ya nuna cewa duk ma'auratan da ke kokarin ƙara danƙon soyayya a ɓangaren jin daɗin juna ya dace su riƙa yin kwanciyar aure mintuna 30 bayan sun tashi daga banci.

Wani kamfanin kula da kiyon lafiya a ƙasar Burtaniya, wanda kwararrun masu binciken lafiya Andy Duckworth da Paul Finnegan suka kafa a 2019 ne ya gano haka.

Rayuwar aure.
Sabon Bincike: Lokacin Da Ya Fi Dacewa Namiji Ya Kwanta Da Matarsa Hoto: tribune
Asali: UGC

Masu binciken sun tara amsoshin mazauna Burtaniya 1,000 kan lokacin da suka fi kaunar yin kwanciyar aure da safe, inda suka gano kashi 1 cikin 4 sun zabi ƙarfe 7:30 na safe.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Wani Abu Ya Fashe, Ya Kama da Wuta a Yankin Birnin Tarayya Abuja

Binciken ya nuna cewa ƙarfe 7:30 na safiya na nufin mintuna 30 bayan sun ta shi daga bacci, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon binciken ya nuna cewa mafi yawan mutane sun zabi ƙarfe 7:00 na safe a matsayin lokacin da suke farkawa daga bacci, haka kuma sun fi son kwanciyar aure da safe misalin ƙarfe 7:30 na safiya.

Kusan kaso 24 na mutanen da kamfanin ya tara ra'ayoyinsu sun zaɓi 7:30 na safe, wasu 'yan kalilan suka ce sai bayan haka suke tarawa da matansu, alal misali kaso 11 sun ce sai karfe 10:30.

"Jima'i da sanyin safiya yana kawo sinadarin Endorphins, wanda ke taimaka wa wajen rage radaɗi a jikin mutum ya inganta yanayi, shiyasa kuke tsintar kanku cikin farin ciki."

Masu binciken sun bai wa mutane shawari

Wannan bincine na cikin 'hanyoyi 12 da zaka bi ka yi rayuwa mai inganci', wanda kwararrun ke zakulo lokacin da mafi kyau al'umma su gudanar da wasu al'amuran rayuwa.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Ta'adda a Kaduna, Da Dama Sun Baƙunci Lahira

Binciken ya shawarci mutane su daure su riƙa farkawa da misalin karfe 7:00 na safe bayan shafe awanni 7 zuwa 9 suna bacci.

Ya kuma ƙara ba da shawarin cewa bayan nan mutum ya fita motsa jiki tsawon mintuna 15, daga nan ya samu jima'i daga bisani ya yi karin kumallo da karfe 7:45 na safe.

Bugu da ƙari, binciken ya yi bayanin cewa karfe 10:00 na safe ne lokacin aiki, 12:45 na rana lokacin cin abinci da kuma 10:00 na dare a amatsayin lokacin bacci.

“Na Fi Karfin Mace Daya”: Wani Mutum Dan Shekara 63 Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Ce Zai Kara Aure

A wani labarin kuma Wani Magidanci mai mata 15 da 'ya'ya sama da 100ya bayyana cewa yana nan yana shirin ƙara Aure.

Mutumin mai shekaru 63 da haihuwa kuma mai ‘ya’ya 107 ya ce ya tabbatar da cewa matansa ba sa kishi tsakaninsu ta hanyar ɓoye yadda yake mu'amala da su.

Kara karanta wannan

An Shiga Damuwa, A Yayin Da Hukumar Kwastam Ke Shirin Hana Shigo Da Kayan Sawa Na Gwanjo Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel