“Na Fi Karfin Mace Daya”: Wani Mutum Dan Shekara 63 Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Ce Zai Kara Aure

“Na Fi Karfin Mace Daya”: Wani Mutum Dan Shekara 63 Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Ce Zai Kara Aure

  • Wani mutum mai suna David Sakayo Kaluhana ɗan garin Malava mai mata 15 ya bayyana cewa ya fi ƙarfin ya tsaya da mata guda ɗaya
  • Mutumin mai shekaru 63 da haihuwa kuma mai ‘ya’ya 107 ya ce ya tabbatar da cewa matansa ba sa kishi tsakaninsu ta hanyar ɓoye yadda yake mu'amala da su
  • Lokacin da fitacciyar kafar yaɗa labarai ta ƙasar Kenya, TUKO.co.ke ta ziyarci gidansa, matansa da ke a gidaje daban-daban sun fito don basu bayanai

Wani mutum mai shekaru 63, David Sakayo Kaluhana, mai mata 15, ya bayyana cewa suna zaune cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.

Mutumin wanda masanin tarihi ne, kuma mahaifi ga yara har guda 107 ya ce ya yanke shawarar auren mata da yawa ne saboda ya fi ƙarfin zama da mace ɗaya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Komawar Shugaba Buhari Nijar Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Mutumin da ke da mata 15 da yara 107 ya ce yana bukatar kari
Mutumin da ke da mata 15 da yara 107 ya ce yana bukatar kari. Hoto: Shiro Mbugua/TUKO.co.ke
Asali: UGC

Zan ƙara aure

Mutumin ya shaidawa shahararriyar kafar yaɗa labarai ta Kenya, TUKO.co.ke, cewa yana tabbatar da cewa ya ciyar da iyalansa dukkansu, wato yaransa da matansa 15 da ke a gidaje daban-daban a ƙauyen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaluhana ya ƙara da cewa yana da wasu matan a ƙasar dake makwaftaka da ƙasar ta Kenya wato Uganda, kuma ya ce har yanzu bai ma gama ba.

A cewarsa:

“Ƙari na nan tafe, ban gama ba haka nan. Ba zan iya bayyana lokacin da zan daina ba, amma nasan cewa muddin ana ba su abinda ya kamata, to fa ba za su yi ƙorafi ba.”

A yayin da ake hirar, matan su kuma suna zauna tare suna ta hira cikin raha a tsakaninsu. Babbar matarsa tana da shekaru 60 a duniya.

Dukansu sun gamsu da rayuwar da muke yi

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Jamhuriyar Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Bayan Na Sauka Daga Mulki, Buhari

Kaluhana ya kuma bayyana cewa matansa sun aminta da irin rayuwar da suke yi a ƙarƙashinsa. Kasancewar shi ne ke basu duk abinda suke buƙata, ya ce yana ƙoƙarin yi wa kowace abinda ya kamata.

Ya ce matarsa ta farko tana da shekaru 49, sannan kuma ƙaramar cikinsu tana da shekaru 23 ne.

Ya ƙara da cewa matarsa da ta fi yawan 'ya'ya itace mai 'ya'ya 16, a yayinda ƙaramar ke da guda 5, wacce a haka ita ce mai yara kaɗan. Ya kuma ce har yanzu bai gama haihuwa ba, yana da sauran yara masu zuwa a gaba.

Wasu matan sun rabu da shi

Sai dai Kaluhana ya bayyana cewa wasu daga cikin matan nasa su biyu sun rabu da shi saboda ba za su iya zaman auren ba.

Ya ce suna tsammanin zai riƙa zuwa wajensu kowane dare wanda hakan ba mai yiwu bane a tsarin da yake yi da sauran matan.

Kara karanta wannan

“Na Tsani Cacar Wasanni”: Yaro Ɗan Shekara 19 Ya Ci N38m Da N450, Mahaifinsa Ya Ce Ya Mayar Da Kuɗin

Matan sun bayyana cewa babu batun kishi a tsakaninsu, sun ce sun riga da sun shagaltu da renon yaransu.

Sannan wasu daga cikinsu sun bayyana cewa babu dalilin da zai sa su tsaya suna kishi tunda dai mijin nasu ya raba musu guraren da za su riƙa yin noma.

Zaku iya kallon hirar a kasa:

Magidanci mai mata 8 zai ginawa yaransa makaranta

A wani labarin makamancin wannan, wani magidanci da ke da mata 8 da yara fiye da 50 ya bayyana cewa zai gina musu makaranta tasu su kaɗai.

Ya bayyana cewa zai ginawa yaran nasa makaranta kusa da gida ne saboda wacce suke zuwa ta yi nisa da inda yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel