Wata Tanka da Ta Ɗauko Man Gas Ta Fashe, Ta Kama da Wuta a Yankin Abuja

Wata Tanka da Ta Ɗauko Man Gas Ta Fashe, Ta Kama da Wuta a Yankin Abuja

  • Wata Tanka makare da Gas ta fashe a yankin birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023
  • Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na dare kuma bisa tilas mutane suka nemi tsira
  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce babu wanda ya musu sakamakon fashewar tankar

Abuja - Babbar motar ɗaukar kaya da ta ɗauko Gas da yawa ta fashe kuma ta kama da wuta a yankin Gwagwa dake birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a da daddare.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa yan jarida cewa Tankar ta yi bindiga da misalin ƙarfe 8:30 na dare a kusa da wani wuri da ake kira Police Junction.

Fashewar Tanka.
Wata Tanka da Ta Ɗauko Man Gas Ta Fashe, Ta Kama da Wuta a Yankin Abuja Hoto: leadershipng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta ce babu wanda zai iya bayyana ɓarnar da ibtila'in ya yi domin baki ɗaya mutanen yankin sun gudu don tsira da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

Mutumin ya ce da yawan mutane sun tsaya can daga nesa suna kallon yadda abun ya faru da wutar da ke ci sakamakon fashewa da tarwatsewar babbar motar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

Hukumar 'yan sanda reshen Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a, SP Josephine Adeh.

Sanarwan ta ce:

"Ranar 9 ga watan Yuni, 2023 da misalin karfe 9:00 na safe Wata babbar mota Tanka ɗauke da Gas ta samu matsala a kusa da makarantar Firamaren Gwagwa a titin Gwagwa zuwa Karmo."
"Ana cikin gyara sai ta fara tartsatsin wuta wanda ya haddasa fashewar Gas, babbar Motar ta kama da wuta. Mun gode Allah babu wanda ya rasa rayuwarsa.
"Lamarin ya faɗa karkashin caji Ofis ɗin Gwagwa bisa jagorancin DPO, wanda ya jagoranci jami'an yan sanda da kuma na hukumar kwana-kwana suka je wurin, suka yi duk mai yuwuwa don dakile wutar."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Dakatar da Ma'aikata Daga Aiki, Ya Tsige Wasu Hadimai Daga Kan Muƙamai

Sanarwan ta ƙara da cewa a halin yanzun hukumar 'yan sanda na ci gaba da bincike don gano asalin abinda ya haddasa fashewar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

A wani rahoton na daban kuma Wata mummunar gobara da ta tashi ta ritsa da ƴan kasuwa da dama a wata babbar kasuwa a birnin Damaturu na jihar Yobe.

Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Juma'a inda ba a samu nasarar kashe ta ba har sai wajen ƙarfe 4:00 na dare.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel