Dakarun Soji Sun Halaka Yan Ta'adda, Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna

Dakarun Soji Sun Halaka Yan Ta'adda, Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna

  • Gwarazan dakarun rundunar sojin Najeriya sun halaka yan ta'adda da dama yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna
  • Hukumar soji ta bayyana cewa 'yan bindiga 6 ne suka bakunci lahira yayin musayar wuta da sojojin Operation Forest Sanity
  • Ta yaba wa sojin bisa wannan nasara kana ta roki al'umma su riƙa agaza wa jami'ai da bayanan sirri kuma a kan lokaci

Kaduna - Dakarun sojin rundunar Operation Forest Sanity da haɗin guiwar jami'ai na musamman daga Hedkwatar tsaro ta ƙasa sun ragargaji yan bindiga a jihar Kaduna.

Vanguard ta rahoto cewa yayin wani samame da suka kai mafakar yan ta'addan, Sojin sun sheƙe yan bindiga 6 a musayar wuta, kana sun kwato makamai daga hannunsu.

Dakarun soji.
Dakarun Soji Sun Halaka Yan Ta'adda, Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, ya ce sojin sun lalata sansanin 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: 'Yan Bindiga Sun Halaka Fitaccen Malami a Babban Birnin Jihar PDP

A sanarwan, Manjo Janar Danmadami ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023, rundunar Soin Opeartion Forest Sanity da haɗin guiwar jami'an hedkwatar tsaro na musamman sun kaddamar da farmaki kan maɓoyar 'yan bindiga a kauyen Maidaro, yankin Giwa a Kaduna."
"Sojin sun gwabza da yan ta'adda yayin samamen kuma garin haka suka sheƙe 'yan ta'adda 6, suka kwato bindigun AK-47 guda 5 da kuma alburusai na musamman guda 192."
"Haka nan sun kwato wasu alburusai masu nauyin 7.62 guda 74 da bindigun AK-47 Magazines guda 47, sai kuma abubuwan fashewa 3, Radio uku, PKM ɗaya da kuma babura 3."

Hukumar soji ta yaba wa jami'an rundunar Operation Forest Sanity bisa wannan nasara da suka samu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Ta kuma buƙaci al'umma su riƙa taimakawa sojoji da bayanan sirri kan ayyukan 'yan ta'adda da sauran miyagu masu aikata muggan laifuka a yankunansu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

'Yan Bindiga Sun Halaka Malamin Coci a Babban Birnin Jihar Edo

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun halaka wani Fadan Coci a babban birnin jihar Edo yayin da yake hanyar dawowa daga wurin aiki.

Wani Rabaran da ke aiki a Cocin Benin Archdiocese, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba shi da hurumin magana kan batun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel