An Yi Bincike, 'Yan Majalisa Sun Umarci a Kama Mutum 54 a Gwamnatin Buhari

An Yi Bincike, 'Yan Majalisa Sun Umarci a Kama Mutum 54 a Gwamnatin Buhari

  • Binciken kudi da kwamitin majalisa ya gudanar, ya jefa wasu hukumomi da ma’aikatu a matsala
  • Kwamitin Hon. Oluwole Oke ya bada shawarar cafke Gwamnan CBN da wasu shugabannin hukumomi
  • Oke yace sun nemi bayanan kudin da aka kashe a ma’aikatun, amma da gan-gan aka ki ba su rahoto

Abuja - Kwamitin da ke binciken asusun gwamnati a majalisar wakilan tarayya, ya bada shawarar a cafke wasu jami’ai da shugabannin hukumomi.

Premium Times a rahoton da ta fitar a daren Juma’a, ta bayyana cewa shawarar tana cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hon. Oluwole Oke ya gabatar.

Kwamitin Hon. Oluwole Okey ya zargi shugabanni hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun gwamnatin tarayyar da kin gabatar da rahoton kudin da suka kashe.

Majalisa ta nemi karin bayani a kan kudin da aka batar tsakanin 2014-2018 da kuma 2019-2021 a ma’aikatun kasar da abin ya shafa, amma sai aka hana ta.

Kara karanta wannan

Ma’aikatar Tarayya ta Bayyana Silar Kai Tauraro D’Banj Wajen Hukumar ICPC

Godwin Emefiele ya shiga uku

Rahoton yace daga cikin wadanda kwamitin ya bukaci jami’an tsaro su kama har da gwamnan babban banki na kasa watau CBN, Mr. Godwin Emefiele.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika ana neman shugabannin kamfanin mai na kasa (NNPC), hukumar kula da cigaban Neja-Delta (NDDC) da RMAFC mai yanka albashin ma’aikata.

Kwamitin ya dogara da sashe na 89(d) na kundin tsarin mulkin kasa, yace za a tursasawa jami’an tsaro su kama wadanda ake nema nan da mako daya.

NNPC.
Shugabannin NNPC a Aso Rock Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Sauran makarantu da hukumomi

Rahoton ya kuma bukaci a hukunta cibiyar lafiya ta FMC Umuahia, Jami’ar tarayya ta Jos, Jami’ar fasaha ta Akure, da jami’ar Ilorin da jami’ar tarayya ta Gusau.

Sauran wadanda za a dauki matakai a kansu su ne: Kwalejin ilmi ta Obudu, jami’ar aikin gona ta Makurdi, FMC Ado Ekiti da Lokoja, da hukumar binciken lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

...Za a hada da Hukumar EFCC

Sannan kwamitin yana zargin an tafka barna a hukumar NIMASA tsakanin 2005 zuwa 2019, don haka ya bukaci jami’an EFCC suyi bincike na musamman.

Haka abin yake ga bankin da ke bada bashin gina gida a Najeriya, za a damka duka shugabanni da darektocin bankin tsakanin 2013 zuwa 2018 ga jami’an EFCC.

Har ila yau, jaridar taace akwai bukatar a kai tsohon shugaban jami’ar gona ta Abeokuta da shugaba mai-ci da tsohon ma’ajinta zuwa gaban hukumar.

Abin bai tsaya a kan su ba, akwai zargin da ke kan NigComSat, ICRC, da dakarun NDLEA.

Ba zan ba mutane kunya ba - Atiku

Rahoto ya zo cewa abubuwan da Gwamnatin Atiku Abubakar za ta fara a tashin farko sun hada da canza fasalin kasa domin a inganta tsaro da tattalin arziki.

Atiku Abubakar yace ya san kan aiki, ya yi alkawari ba zai ba mutane kunya ba kamar yadda a cewarsa gwamnatin APC mai-ci tayi bayan shekaru bakwai.

Kara karanta wannan

An Samu Karin Talauci Duk Da Tallafin N3.5tn DaGwamnatin Tarayya Ta Bayar

Asali: Legit.ng

Online view pixel