Lai Muhammad Yace Gwamnatin Buhari Ta Tseratar Da 'Yan Nigeria Daga Yunwa

Lai Muhammad Yace Gwamnatin Buhari Ta Tseratar Da 'Yan Nigeria Daga Yunwa

  • Lai Muhammadu wanda yake a matsayin ministan labarai hadi da al'adu ya ce ya kamata a jinjinawa buhari sabida kubutar da kasar nan da yayi daga yunwa
  • A wata k'iddiga da hukumar NBC tayi, ya nuna akwai 'yan Nigeria kimanin Mutum miliyan 133 dake fama da talauci
  • A wani sakamakon bincike da hukumar kula da lafiya ta duniya ta fitar ya nuna Nigerai na gaba-gaba wajen yara masu fama da cutar yunwa

Abuja: Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cimma nasarar samar da abincin da kuma bunkasar kayyayakin da aka 'kera a Najeriya.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar alhamis a abuja kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito

A cewar Mohammed, duk da rikice-rikicen da suka shafi tsadar rayuwa, gwamnati tayi kyakyawan aiki tun bayan hawanta kan karagar mulki a fannin dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Fadi Adadin Biliyoyin da ta Karbe a Hannun Barayi a Shekarar nan

"Na tabbata da yawa da ga cikinmu sun ga bidiyon manyan kantunan da ba komai a cikinsu a kasahshen yammacin duniya, musamman a lokacin Covid-19.
“Tun kafin wannan rikece-rikice shugaba Buhariya ya sha ya sha gargadin ‘yan Nigeria da su noma abinda zasu ci daga daga abinda suka samar.
"Da yawa basu fahimci muhimmancin gargadin ba da kuma alfanunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"To Sakamakon wannan Magana tasa, 'yan Najeriya su ka shiga taitayinsu kuma hakan ya ceci Nigeria, musamman a lokacin da aka dad'e ana kullen korona da lokacin da k'asashen duniya daina fitar da kayyakinsu zuwa wasu k'asashen."

Lai Muhammad Yace

Lai Muhammad
Lai Muhammad Yace Gwamnatin Buhari Ta Tseratar Da 'Yan Nigeria Daga Yunwa Hoto: The Cable
Asali: UGC

Mun Samar Da Taki Dan Noma Inji Minista

A cewarsa, yawan takin da ake hadawa na zamani a kasar ya karu zuwa kashi 10, haka kuma an samu karuwar masana’antar sarrafa shinkafa da injinan ni'kanta, wanda ya taimaka wajen samar da wadataccen abinci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kassara 'yan ta'adda, sun ragargajiya maboyar 'yan bindigaa dazukan wata jiha

“idan ka ziyarci kasuwannin mu da kantunanmu, abinda zaka gani galibi su ne kayayyakin da aka yi a Nigeria. Wannan babban ci gaba ne a kankanin lokaci."

Da yake karin haske game da tsadar kayan abinci, ministan ya bada tabbacin cewa yayin da k’asar nan ta k’ara himma wajen samar da abinci a cikin gida to farashin kayan abinci zasu fara raguwa.

"A yanzu ya zama dole a yaba da nasarar da muka samu ta samar da abinci da inganta kayyyakin gida," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel