Duk Da Tallafi Kudi Kusan Tirilian Uku Da Digo Biyar Har Yanzu Akwai Talauci Da Yawa A Nigeria

Duk Da Tallafi Kudi Kusan Tirilian Uku Da Digo Biyar Har Yanzu Akwai Talauci Da Yawa A Nigeria

  • Jaridar Leadership ta gano yawan matalauta na karuwa a Nigeria, dukka da yunkurin gwamnatin na rage yawan matalautan
  • Kimanin mutum miliyan 133 ne ke fama da talauci a Nigeria a wata kiddiga da hukumar kiddiga ta kasa NBC, tayi
  • Kayyyakin Masarufi, more rayuwa da sauran abubuwa rayuwar yau da kullum na kara tsefewa da tsada a kasuwannin fadin kasar

Nigeria: A wani nazari da jaridar LEADERSHIP ta yi, ta gano cewa, gwamnatin tarayya ta kashe kimanin naira tiriliyan 3.5 wajen samar da ayyukan yi ga al’umma da kuma kudirin rage radadin talauci amma ga dukkan alamu talauci na karuwa.

Sadiya Umar Farouk
Duk Da Tallafi Kudi Kusan Tirilian Uku Da Digo Biyar Har Yanzu Akwai Talauci Da Yawa A Nigeria Hoto: Leadership
Asali: UGC

Wani rahoto na baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna kimanin ‘yan Najeriya miliyan 133 ke cikin talauci, duk da cewa gwamnati na kashe Naira biliyan 500 a duk shekara kan tsarin

Kara karanta wannan

Yaki da rashawa: Yadda EFCC ta yi gwanjon motocin da ta kwace a hannun mahandama a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dangane da yadda ake kashe Naira biliyan 500 a duk shekara kan tsare-tsaren tallafawa al’umma, Zuwa yanzu kudin da aka kashe ya kai Naira tiriliyan 3.5 a cikin shekaru bakwai tun shekarar 2015.

A farkon wannan shekarar ma, an ruwaito ministar harkokin jin kai da kula da walwalar al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta ce ana kashe dala biliyan 1 duk shekara wajen aiwatar da wasu shirin-shiryen NSIP.

Ministan wanda babban sakataren ma’aikatar Nura Alkali ya wakilce ta a wani biki da aka gudanar a watan Janairu, 2022, ya ce:

“Tun daga hawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, gwamnatin tarayya ta kara maida hankali wajen inganta halin da mutane ke ciki musamman ma Talakawa da marasa galihu a kasar".
“A dalilin haka yasa gwamnati yanke hukunchin fara shirin yin NSIP, a matsayin dabarun inganta jama’a. NSIP na daya daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin shugaba muhammadu Buhari yayi, wanda akalla duk kwatar shekara ana kashe kudade sama da biliyan guda wajen yin wannan shirin"

Kara karanta wannan

Gobara Ta Ƙona Tankokin Dizal 5 A Kano, Lita 20,400 Na Dizal Ya Ƙone

Yayin da hauhawar farashin kayayyaki da kuma yanayin gudanar da harkokin kasuwanci ke kara ta'azzara a kasar nan, haka ma talauci ke baje koli shima a kasar nan.

Mai Masana Suke Cewa Game Da Shirin Gwamnati Na Fitar Da 'Yan Nigeria Daga K'angin Rad'ad'in Talauci

Wasu masana da suka zanta da LEADERSHIP a hirarsu daban-daban, sun yi tsokaci iri-iri kan batun.

Darakta-Janar na Cibiyar Kasuwanci da Masana'antu ta Legas (LCCI), Dr. Chinyere Almona, ya ce:

"Shirye-shiryen gwamnati na rage rad'ad'in talauci sun yi tasiri yayin da tattalin arzikin kasar ya samu murmurewa daga koma bayan tattalin arziki da annobar COVID-19 ta haifar a kasar a shekarar 2020".

A nasa bangaren, babban jami’in cibiyar bunkasa sana’o’in hannu (CPPE), Dokta Muda Yusuf ya ce:

“Shirin ba da agajin ga jama’a ya yi tasiri kamar a shirin gwamnatin na N-Power, shirin bankin Nigeria CBN ga manoma da sauransu, amma kalubalen shi ne girman matsalar ta yi yawa matuka.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kama wasu kudade N19.5 a hannun abokan 'yan bindiga 5 a Arewa

Yusuf ya kara da cewa cewa:

“Al'ummar da ke fama da matsanancin talauci a Nigeria sun miliyan 133, kuma ina da tabbacin duk tallafin da shirye-shiryen gwamnatin tarayya na rage rad'ad'in talaucin bai kai yawan mutane miliyan uku ba. to ka ga maganar baza'ace sunyi yunk'urin azo a gani ba. "

Ya kara da cewa, akwai bukatar gwamnati ta samar da wani yanayi da ‘yan kasa da kansu za su magance matsalar talauci, yana mai cewa,

“Ya kamata a samar da hanyar da yan kasar zasu magancewa kansu matsaloli da yawa ba komai sai gwamnati ta shiga ba".

“Misali, yawan talauci da rashin tsaro da ya ta'zzara, wannan matsalar ai kaga kudi ne maganinta ba.”

Ya yi kira da a samar da yanayi mai dorewa a fannin ilimi, lafiya da sauran sassan tattalin arziki, yana mai cewa:

“Samar da hanyoyin zasu kawo hanyar magance matsalar talauci a kasar nan. Da kuma batun habaka tattalin arziki mai dorewa. ”

Kara karanta wannan

Wani Jami'in Hukumar Shige Da Fice Ya Rasa Karin Girma Sakamakon Kai Karar Ogansa

Haka kuma, shugaban kididdigar cibiyoyin kudi na Agusto & Co, Ayokunle Olubunmi, ya lura cewa:

"Da dama daga cikin shirye-shiryen rage rad'ad'in talauci da gwamnatocin da aka kafa ba su mayar da hankali kan fitar da mutane daga k'angin talauci ba".

A cewarsa, an tsara tsarin da aiwatar da shirye-shiryen ne don ba da agaji na wucin gadi ga wadanda suka ci gajiyar shirin kurum.

“Ko da yake ana kiran shi kudi na taimakon jama’a, idan aka duba tsare-tsare da yadda ake aiwatar da su, abin da su ke yi shi ne bayar da tallafi. Idan gwamnati na maganar rage radadin talauci, akwai bukatar a samar da tsarin da a zahiri mutane za su yi sana’o’in dogaro da kai su samu kudin shiga".

Mai Kungiyoyin Sa Kai Ke Cewa Game Da Batun Talauci A Nigeria

Kungiyar Kare Hakkin Tattalin Arziki (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kafa kwamitin bincike don bincikar kashe kudaden da tsakanin 2015 da 2022."

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

SERAP ta kuma bukace shi da a tabbatar da cewa an buga sakamakon binciken irin wannan rahotan a ko’ina, tana mai kara cewa :

Duk wanda ake zargi da aikata almundahana, da almubazzaranci da dukiyar al’umma to ya fuskanci hukunci kamar yadda ya dace.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan Nuwamba 19, 2022 mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce:

“Rahoton ya nuna cewa an tauye hakkin jama’a sosai, da kuma rashin kishinyasa ake kara samun talauci a tsakanin 'yan kasa kuma ake take hakkin dan Adam.”

SERAP ta kara da cewa:

“Rahoton cewa ‘yan Najeriya miliyan 133 matalauta ne, ya nuna almundahana, cin hanci da rashawa sukayiwa gwamnati katutu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel