Ma’aikatar Tarayya ta Bayyana Silar Kai Tauraro D’Banj Wajen Hukumar ICPC

Ma’aikatar Tarayya ta Bayyana Silar Kai Tauraro D’Banj Wajen Hukumar ICPC

Ma’aikatar jin-kai, bada agajin gaggawa da cigaban al’umma ta tabbatar da cafke D’Banj da aka yi

Gwamnatin tarayya tana zargin ana tafka badakala a karkashin N-Power, don haka ta gayyato ICPC

Sakataren din-din-din na ma’aikatar yace ba za suyi wa jami’an ICPC katsalandan a bincikensu ba

Abuja - Ma’aikatar jin-kai, bada agajin gaggawa da cigaban al’umma tace ita ta gayyaci hukumar ICPC domin ta binciki badakalar da ke N-Power.

Jaridar Daily Trust tace a dalilin zargin barnar da ake tafkawa aka nemi jami’an da ke yaki da cin hanci da rashawa suyi bincike, har aka tsare D’Banj.

Ana tuhumar mawakin da hada-kai da wasu jami’an gwamnatin tarayya wajen shigo da ma’aikatan bogi a cikin wannan tsari domin a saci kudi.

Bayan an biya wadannan ma’aikatan bogi, su kuma sai su tura kudin zuwa wani asusu da ake zargin yana da alaka da fitaccen mawakin na Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan Sanusi II da Iyalansa a Landan Wurin Taya Diyarsa Murnar Kammala Digiri na 2 a Fannin Shari’a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magana ta je ga Jami'an ICPC

Sanarwar da aka fitar a ranar Laraba ya nuna cewa bayan an fahimci ana wawurar kudi da sunan tsarin, sai aka ankarar da ICPC domin a binciki lamarin.

Kafin nan, an yi duk kokarin da za a iya wajen ganin an fatattaki ma’aikatan bogi daga tsarin.

Ma'aikata tayi magana

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar jin-kai, agajin gaggawa da cigaban al’umma, Dr. Nasir Sani-Gwarzo ya kyankyasa haka da ya zanta da su This Day.

Dr. Nasir Sani-Gwarzo yace sun san da an gayyaci wasu mutane domin yi masu tambayoyi, jami’in yake cewa ba za su tsomawa ICPC bakinsu ba.

D'Banj
Hukumar ICPC na binciken D'Banj Hoto: notjustok.com
Asali: UGC

Shirin NSIP da aka fito da shi

A karkashin tsarin NSIP da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo, ana ciyar da ‘yan makaranta ta NHGSFP, ana rabawa marasa karfi kudi ta CCT.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Har ila yau, a sanadiyyar tsarina kwai shirin GEEP da aka shigo da shi domin inganta rayuwar jama’a, baya ga haka matasa suna amfana da N-Power.

A karshen sanarwar, jaridar tace an tabbatarwa jama’a masu cin moriyar N-Power za su cigaba da amfana da tsarin har zuwa lokacin da za a yaye su.

A gefe guda, Lauyan da ya tsayawa mawakin ya koka. Oladapo Oyebanjo yace babu abin da ya hada mawakin daga zargin da hukuma take yi masa.

Sojoji na zubar da ciki?

Daga 2013 zuwa yau, wani rahoto daga Reuters yace akwai mata 10, 000 da sojoji su ka zubar masu da cikin da suke dauke da shi, da karfi-da yaji.

Matan sun samu ciki ne a wajen ‘Yan ta'addan Boko Haram, don haka jami’an tsaron ke gudun a sake haifo yaran ‘Yan ta’addan da ke kashe mutane.

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya Tayi Magana a Kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Za Ta Goyi Baya

Asali: Legit.ng

Online view pixel