Atiku Ya Bayyana Abubuwan da Zai Tunkara a Ranar da Ya Fara Shiga Fadar Aso Rock

Atiku Ya Bayyana Abubuwan da Zai Tunkara a Ranar da Ya Fara Shiga Fadar Aso Rock

  • Jirgin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a 2023 ya shirya gagarumin kamfe domin Atiku Abubakar a Osun
  • Da ya mike domin yi wa mutanen jihar Osun bayani, Atiku Abubakar yace zai kawo sauyi a fasalin tsarin kasa
  • Da zarar ya dare kujerar shugaban kasa a 2023, Atiku ya yi alkawarin fara aiki domin magance matsalolin jama'a

Osun - Atiku Abubakar wanda shi ne ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, yace zai yaki rashin tsaro da sauran matsalolin Najeriya.

Premium Times ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana mai shan alwashin da zarar ya shiga ofis, to zai fara aiwatar da tsare-tsaren canza fasalin kasa.

Da yake bayani a wajen kamfe a garin Osogbo a jihar Osun, ‘dan takaran yace idan dai ya ci zaben 2023, aka rantsar da shi, to zai kawo sauye-sauye.

Atiku yake cewa babu abin da ya dame shi illa kawo karshen matsalolin da suka addabi Najeriya.

Da zafi-zafi a kan bugi karfe

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ba bakon fadar Aso Villa ba ne, yace daga ranar farko zai shiga aiki domin cika alkawarin da ya dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Burin da ke gabanmu kawai shi ne mu ga karshen matsalolin kasar nan na rashin tsaro, rashin hadin-kai, matsin tattalin arziki, rashin ayyukan yi da makoma ta hanyar yi wa tsarin kasa garambawul.
Atiku Abubakar a Legas
Atiku Abubakar a Kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Twitter

Nayi maku alkawarin cewa daga ranar farko da na shiga ofis zan fara aiwatar da su.

- Atiku Abubakar

Atiku: A zabi PDP a Osun a 2023

Ina kira gare ku, da ku fito kwanku da kwarkwatarku kamar yadda kuka yi a zaben Gwamna, ku zabi jam’iyyar PDP a babban zabe.
Ta haka ne kurum makomarku da ta ‘ya ‘yanku za tayi kyau. Ba za mu ba ba ku kunya ba, mu ba APC ba ne, mun yi an gani a baya.

Mun san kan aiki, muna da abin da ake bukata domin kawo gyara, ba yau muka san shugabanci ba."

- Atiku Abubakar

A jawabinsa, ‘dan takaran na PDP yace ba zai ci amanar jama’a ba, muddin suka ba shi kuri’arsu a zaben shugaban kasar da za ayi a farkon shekarar badi.

Vanguard ta rahoto Gwamna Ademola Adeleke yana kira ga mutanen jiharsa da su zabi Atiku Abubakar domin shi ya dacewa ya mulki Najeriya a 2023.

Na gama takara - GEJ

Rahoto ya zo cewa shi kuma Goodluck Jonathan yana ganin ya fara yawon neman takarar shugabancin kasa yanzu a Najeriya, bata sunansa zai yi.

A littafin da aka rubuta na tarihin Obioma Onwuzurumba, Jonathan ya yi bayanin yadda ya ji da ake rade-radin zai nemi mulki a APC a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel