Martanin 'yan Najeriya bayan da Aisha Buhari ta janye karar da ta shigar kan Aminu Muhammad

Martanin 'yan Najeriya bayan da Aisha Buhari ta janye karar da ta shigar kan Aminu Muhammad

  • Bayan da aka kai ruwa rana kan batun kame matashi Aminu da ya yiwa Aisha Buhari rashin kunya, ta janye karar da ta shigar a kansa
  • An shigar da karar Aminu, inda aka nemi ya ya amsa wasu laifuka da ake zarginsa dasu na bata sunan Aisha Buhari
  • Ya zuwa yanzu dai ba a sako AMinu ba, amma ana kyautata zaton lamura sun yi sauki, ga dai martanin jama'a game da haka

Labari ya iso mu cewa, Aisha Buhari, uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta janye wata karar da ta shigar kan wani dalibin da ake zargin ya yi mata gatsali a shafin sada zumunta.

Jim kadan bayan samun labarin nan daga wani lauyansa, C.K Agu, jama'ar Twitter suka fara bayyana ra'ayoyinsu kan abin da suka ji bayan janye wannan kara.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Dai Aminu Zai Gana Da Shugaba Buhari A Villa Yau, Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Data Shigar

Duk da sanar da janye karar, ba mu samu labarin ko an sako matashin baamma akwai yiwuwar janye ta haifar da da mai ido ga Aminu Muhammadu.

An janye karar da aka shigar kan matashin da ya zagi Aisha Buahri
Martanin 'yan Najeriya bayan da Aisha Buhari ta janye karar da ta shigar kan Aminu Muhammad | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Shinfida ga abin da ya faru

A tun farko mun kawo muku rahoton yadda aka kama wani matashi, Aminu Muhammad, dalibi a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, inda aka zarce dashi Abuja don amsa laifin zagin uwar gidan shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan lamari ya haifar cece-kuce a Najeriya, inda kungiyoyi da 'yan gwagwarmaya suka bayyana fushi tare neman a sako matashin.

Ana zargin matashin ne da hawa shafin Twitter tare da cewa, Aisha Buhari ta lashi 'yan kudaden talakawa ta teba.

Martanin 'yan Twitter bayan janye kara

A kasa, mun tattaro muku ra'ayoyin jama'a kan batun janye karar da uwar gidan shugaban kas ata shigar.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

@muhdabdullahi22 yace:

"Sakinshi Yazama Dole Kuma Yanzu Kinga Kinzama Mujiya Acikin Talakawa Donhaka Abinda Kikayiwa Yaronnan Bamu Yafemikiba,Kuma Dasannu Zaki Girbi Ko Ince Zaku Girbi Abinda Kuka Shuka Awannan Azzalimar Gwamnatin Taku Tir….."

@Omar_fharuq yace:

"Kinyi abinda ya kamata wlh, shikuma kinga gobe aiya sake tunda dan iska ne shi.
"Karku manta zagin shuwagabanni haramun ne kuma koba hakaba ai tayi uwa dashi ma."

@ibrahimmaazzam3 yace:

"To yanzu hukunci na adalci zakibiyashi dala dubu goma sannanki auramasa yar autarki fakat."

@Dixie_slim yace:

"Yanzu ai sai ya shiga taitayin sa. Ya gane cewa ba komai yaga dama zai rubuta a kafar sada zumunta ba. Allah ya kiyaye na gaba."

@RbbMusa yace:

"Gaskiya talauci akwai ƙarfin tsiya daga ƙarshe dai mu talakawa munyi nasara.‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️."

@AliyuSh39506567 yace:

"A dokokin nigeria an bawa first lady kotun tafi da gidanka? domin ta kulle bawan Allah sama da kwana 10 tare da wulakanci da duka, yanzu na kara tabbatarwa ba doka akan iyalan shugabanni sannan ya zama dole ayi mana bayani akan dukiyar kasarmu dan me ake fama da mugun talauci?"

Kara karanta wannan

Wani Jami'in Hukumar Shige Da Fice Ya Rasa Karin Girma Sakamakon Kai Karar Ogansa

A baya mun kawo cikakken rahoton yadda Aisha Buhari ta janye wannan kara a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel