Atiku Yace Jam'iyyar APC Fa Dama Ba Abinda Zasu Iya Yiwa Nigeria

Atiku Yace Jam'iyyar APC Fa Dama Ba Abinda Zasu Iya Yiwa Nigeria

  • Yan Siyasa na suka ko jefan junan su da maganganu marasa dadi wanda wani lokacin ma takan kai ga zarafi ko karya
  • Zabe na kara karatowa a Nigeria Inda 'Yan siyasa ke kara wukar sukar su da kuma neman magoya bayan da zasu basu kuri'a
  • Hukumar zaben Nigeria tace a shirye take kan Baban Zaben kasar da za'ayi a watan Fabrairun shekara mai kamawa

Jigo a jam'iyyar PDP, kuma daya daga cikin wanda suke zawarcin kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, a jiya dan takarar ya nuna jam’iyyar APC mai Mulki ta barnatar da shekaru takwas wanda suke da muhimmaci ga yan wajen bunkasa kasa amma da tayi komai ba.

Da yake bayanin shekaru da Tsohon Janar din sojan ya shafe a mulki wato Buhari, ya bayyana ta a matsayin mafi tabarbarewar mulki a Nigeria,kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa

Kara karanta wannan

Ku zabi mijina, ya fi Tinubu: Matar Atiku ta fadi dalilan da za su sa Yarbawa su zabi PDP

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP da ya ke jawabi a lokacin yakin neman zabensa na shugaban a jihar Ondo Kudu maso.

Atiku
Atiku Yace Jam'iyyar APC Fa Dama Ba Abinda Zasu Iya Yiwa Nigeria
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa,

“Ba za ka kwatanta abin da PDP ta yi a cikin shekaru 16 da abin da APC ta yi a cikin shekaru takwas ba, ba su tabuka komai ba.

Yayin da yake nuna rashin aikin yi da talauci a fadin kasar nan, Atiku ya bayyana cewa gazawar gwamnati mai ci wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasa ya tabbatar da gazawar gwamnatin Buhari.

A cewarsa,

“wasa ne ma ace za’a kwatanta abinda gwamnatin PDP tayi tsawon shekaru 16 da wannan gwammnatin da tai shekaru8.

Abubuwa Da Dan Takarar Ya ce

Ya bayyana fatansa cewa idan jam’iyyarsa ta PDP ta yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa, gwamnatinsa za ta kawo

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

Yayin da yake yabawa jam'iyyar PDP a jihar Ondo bisa samun mafi yawan kuri'u a yankin Kudu maso Yamma a 2019, dan takarar shugaban kasa ya bukace su da su maimaita irin wannan a zabe mai zuwa.

Kamar yadda yake cewa

“Mun fara gangamin yakin neman zabenmu ne daga jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma. Da gangan ne na nuna muku abubuwan da kuka yi mana a zaben da ya gabata a 2019 saboda mun yaba.

Ya Ci gaba da cewa:

"Idan ku ka sake ba mu kuri'a, za mu kawo karshen rashin tsaro, za mu inganta dukkan hanyoyin zuwa Ondo da zuwa sauran sassan kasar nan."

Atiku ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ta ware dala biliyan 10 domin karfafa matasa kamara yadda yake a a cikin takardar manufofin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel