Kotu Ta Hana ‘Dan Takaran Gwamna, Mutane 26 Masu Harin Zuwa Majalisa Yin Takara

Kotu Ta Hana ‘Dan Takaran Gwamna, Mutane 26 Masu Harin Zuwa Majalisa Yin Takara

  • Jam’iyyar Labour Party tayi galaba a kan ‘Yan takaran African Democratic Congress a jihar Ogun
  • Wani Lauya ya kalubalanci takarar da ADC ta ba Biyi Otegbeye da masu neman kujerar ‘Yan Majalisa
  • Kotu ta gamsu cewa Jam’iyyar ADC ba ta shirya zaben tsaida gwani ba, kuma ta bada tutocin takara

A wata shari’a da aka zartar a babban kotun tarayya mai zama a garin Abeokuta, an hana Biyi Otegbeye shiga takarar gwamna a jam’iyyar ADC.

Daily Trust ta fitar da rahoto a yammacin yau cewa Akintayo Aluko ya rusa takarar wanda aka tsaida Gwamna da duka ‘yan majalisar dokokin jiha.

Hukuncin yana nufin Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba ta da ‘dan takaran Gwamna da na ‘yan majalisar dokoki 26 a jihar Ogun.

Jam’iyyar adawa ta Labour Party ta shigar da kara a kotu a kan cewa an saba ka’ida doka wajen tsaida wadanda za suyi wa ADC takara a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Barakar Tashin Hankali Ta Kunno Kai a Tafiyar Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023

Yaushe aka yi zaben gwani?

A karshen zaman da aka yi, Akintayo Aluko ya zartar da cewa hukumar zabe na kasa watau INEC ba ta san da zaben tsaida gwanin da ADC ta shirya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban kotun tarayyar tace an sabawa dokar zabe na kasa wajen tsaida ‘yan takaran da ake kara.

'Yan APC
Taron kamfe a Ogun Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

The Nation tace Aluko ya gamsu Otegbeye da sauran mutane 26 da ake shari’a da su ba asalin ‘yan takara ba ne, don haka aka bukaci INEC ta hana su takara.

Martanin Lauyoyin LP da ADC

Lauyan da ya tsayawa LP wajen shigar da karar, Monday Mawah ya ji dadin hukuncin da aka zartar, ya fadawa manema labarai abin yin farin ciki ne.

Monday Mawah yake cewa sun kalubalanci hukumar INEC da ta biyewa hukumar INEC wajen amsar ‘yan takaran da ba su samu tikiti ta hanyar halal ba.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Kaddamar da Gangamin Kamfen din APC a Gaya

Shi kuma Tunde Falola wanda ya kare ‘yan takaran ADC a kotu ya nuna za su duba hukuncin da Alkali ya yi, idan ta kama zai su tafi kotun daukaka kara.

Wanene Biyi Otegbeye?

Ana zargin cewa tsohon Gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun ne ya daurewa Biyi Otegbeye gindi domin ya jarraba sa’arsa a kan Gwamna mai-ci.

Kwanaki an ji labari tsohon gwamnan na Ogun, Ibikunle Amosun yace ba zai marawa jam’iyyar APC baya a zaben 2023 ba saboda rikicin cikin gida.

A zaben Shugaban kasa, Sanatan Ogun ta tsakiya yana goyon bayan Bola Tinubu 100% bisa 100%, amma zai yaki tazarcen Gwamna Dapo Abiodun a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel