An Yi Asarar Rayuka Yayin da Rikici Ya Kaure Tsakanin Sojoji da Wasu Matasa

An Yi Asarar Rayuka Yayin da Rikici Ya Kaure Tsakanin Sojoji da Wasu Matasa

  • An rasa gaskiyar lamarin yayin da aka samu sabani tsakanin mazauna garin Oguta da sojojin Najeriya
  • Mazaunan yankin a jihar Imo sun ce sojojin ne suka duro masu, sai suka shiga buda masu wuta haka kurum
  • Wani babban jami’in sojojin kasa ya karyata wannan batu, yace matasan suka tsokano su, su na bakin aiki

Imo - Mutane da-dama ake zargin sun hallaka yayin da matasan Izombe a garin Oguta a jihar Imo, suka yi rigima da dakarun sojojin Najeriya.

The Nation ta kawo rahoto a safiyar Talata, 8 ga watan Nuwamba 2022 cewa mutane sun tafi barzahu a sanadiyyar karon-battar da aka yi a Jihar.

Yayin da dakarun bataliya ta 34 Artillery da ke Obinze ta je karamar hukumar Oguta domin maganin masu tada zaune tsaye, sai rikici ya kaure.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

Kisan wani direban kamfanin Dangote da ake zargin matasan garin sun yi, ya jawo aka aika rundunar sojoji zuwa yankin domin kawo zaman lafiya.

An kashe Direban Dangote

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi wa direban motar Dangote kisan gilla, don haka jami’an sojoji suka tsaurara matakai domin a kare rayuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust tace an ji harbe-harbe a lokacin da matasan suka kai wa motocin jami’an sojojin hari. Wani mazaunin yankin yace sojoji ne suka fara harbi.

Sojoji
Motar wasu Sojojin Kasa Hoto: @beegeaglesblog
Asali: Twitter

Majiyar tace daga shiga garin ne jami’an sojoji suka shiga harba bindigogi babu gaira-babu dalili, an zargi jami’an tsaron da yi wa garin Oguta kutse.

...Ba haka abin yake ba - Sojoji

Da aka tuntubi shugaban bataliyar sojojin kasan, Kyaftin Joseph Akubo ya shaidawa jaridar Tribune cewa ba jami’an tsaron suka fara buda wuta ba.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

Kyaftin Joseph Akubo yace matasan ne suka aukawa sojojin da aka tura rangadi a sakamakon ta’adin da aka samu labarin ana fama da shi a yankin.

Babban jami’in bai iya bayyana adadin mutanen da aka rasa ko aka yi wa rauni ba, ya tabbatar da cewa har zuwa lokacin matasan na kai wa sojoji hari.

Ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan takaddama a yakin kudu maso gabasin Najeriya ba, inda 'yan IPOB suka yi karfi a wasu jihohi.

NDLEA ta kama Makaho da wiwi

A makon nan aka ji labari NDLEA ta kama makaho daga Jamhuriyar Nijar mai shekaru 52 da dansa ‘dan shekaru 30 dauke da tabar wiwi da exol-5.

Kakakin Hukumar NDLEA Femi Babafemi yace sun cafke mutanen ne a titin jihar Katsina a hanyarsu ta komawa Nijar, asalinsu 'Yan Damagaram ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel