An Harbe Fitaccen Dan Bindigan da Ya Addabi Jama’a, Bada a Jihar Zamfara

An Harbe Fitaccen Dan Bindigan da Ya Addabi Jama’a, Bada a Jihar Zamfara

  • An hallaka wnai kasurgumin dan bindigan da ya addabi al'ummomin jihar Zamafara a Arewa maso Yammacin Najeriya
  • An kuma kwato wasu makamai da kayayyaki masu daraja daga wasu 'yan bindigan da aka fatattaka a yankin
  • An bukaci mazauna a yankunan jihar da su ci gaba da tuntubar jami'an tsaro kan motsin 'yan ta'adda

Jihar Zamfara - Kasurgumin dan bindigan da ya addabi al'umma mai suna Bada ya gamu da ajalinsa a hannun sojoji yayin da ya kai farmaki kan manoma a yankin Yar Tashar a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Daraktan yada labarai na gidan soja, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, PM News ta ruwaito

Danmadami ya bayyana cewa, kasurgumin dan bindigan ya mutu ne a fafatawar da ya yi da jami'an sojoji bayan da suka samu kiran neman agaji daga manoman da ke girbin amfanin gona a yankin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Lokacin Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Titin Kaduna-Abuja

An hallaka kasurgumin dan bindigan da ya addabi jama'ar Zamfara
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan da Ya Addabi Jama’a, Bada a Jihar Zamfara | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A cewarsa, an ce Bada ya farmaki kasuwar kauyen Yar Tashar kuma ya kashe wani manomi a ranar 13 ga watan Oktoba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda sojoji suka amsa kiran mazauna kauye

Ya kara da cewa, sojoji a ranar 6 ga watan Nuwamba sun amsa kiran mutanen kauyen Gamraki a gundumar Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu, inda suka ceto mutanen da aka sace.

Hakazalika, ya ce an hallaka wani dan bindiga yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga. An kwato makamai da dama daga hannunsu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce:

"Sojoji sun kwato babur guda daya, wasu makamai da kayayyaki masu daraja.
"Babban kwamandan sojoji ya yabawa rundunar Operation Hadarin Daji kuma ya kara wa mazauna yankin kwarin gwiwar taimakawa jami'ai da bayanai sahihai a kan lokaci na motsin 'yan ta'adda."

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

'Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sanya Wa Manoma Haraji a Jihar Neja

A wani labarin, manoman yankin Atabo da yankunan da ke zagaye da yankin a karamar hukumar Magama ta jihar Neja sun shiga firgici biyo bayan barazanar da 'yan bindiga ke yi na sanya musu haraji.

A cewar rahoton Daily Post, 'yan bindigan na kokarin sanya wannan haraji ne kafin ba manoma damar fara girbin amfanin gona na noman rani da suka yi.

An tattaro cewa, 'yan bindiga sun mamaye yankin Atabo a ranar Talata, sun yi awon gaba da hakimin yankin, Alhaji Mairabo da wani kanensa da ake kira Usman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel