Gwamna Wike Ya Hadu Da Buhari A Wurin Wani Muhimmin Taro A Abuja

Gwamna Wike Ya Hadu Da Buhari A Wurin Wani Muhimmin Taro A Abuja

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers yana cigaba da bawa mutane mamaki, musamman tun bayan rikicinsa da Atiku Abubakar
  • Gwamnan na Jihar Rivers a lokuta da dama ana sha ganinsa da jiga-jigan jam'iyyar APC a Najeriya da kasasashen waje
  • Wike ya sake bawa yan Najeriya mamaki a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, lokacin da ya halarci rantsar da alkalai da Shugaba Buhari ya yi a Abuja

FCT, Abuja - Yan Najeriya sun yi mamakin ganin Gwamna Nyesom Wike yayin rantsar da alkalai a Abuja da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba.

Baya ga halarcin, gwamnatin jihar Rivers karkashin Gwamna Wike, ya bada tallafin N500m don ginin ofishin kungiyar, a cewar shugaban kungiyar alkalan, Wole Olanipekun (SAN), rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Ina Tare Da Wike, Ko Dazu Muna Landan: Ortom Ya Karyata Hadiminsa

Wike da Buhari
Gwamna Wike Ya Hadu Da Buhari A Wurin Wani Muhimmin Taro A Abuja. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin wadanda suka halarci taron har da Babban Alkalin Alkalan Najeriya, Mai sharia Olukayode Ariwoola, da Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN.

Sananen abu ne cewa gwamnan na Rivers na cikin manyan masu sukar gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Amma, Wike cikin sanarwar da kakakinsa, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana kalaman da aka danganta da Lamido a matsayin abin kyama da raini.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

A wani rahoton, Gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel