2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

  • Gwamnonin PDP wadanda ke goyon bayan Wike, an rahoto cewa za su gana da Atiku a karshen mako kan rikicin jam'iyyar
  • Gwamnonin za su gabatarwa Atiku wasu sharruda da zai cika musu idan yana son goyon bayansu ga takarar shugaban kasarsa
  • Daga cikin sharrudan, gwamnonin wai suna son Atiku ya amince cewa ba zai yi tazarce ba idan ya zama shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Atiku tare da jiga-jigan PDP.
2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar da ba a bayyana sunansa ba kuma ya lissafo sharruda da gwamnonin ke son Atiku ya amince da su kafin su goyi bayansa.

Na farko, sun ce dole Atiku ya amince wa'adi daya kawai zai yi idan ya ci zaben shugaban kasa.

Sauran sharrudan, a cewar majiyar suna da alaka da raba mukaman siyasa da sake rabon ofisoshin jam'iyya zuwa yankuna.

"Eh, da gaske ne. Za mu yi taro dan takarar shugaban kasa kuma za mu gabatar masa da sharrudan mu.
"Gwamna Wike ya bamu izini - kuma muna fatan za mu cimma matsaya a karshe.
"Daya daga cikin sharrudan da shi (Atiku) dole ya amince da su shine yin wa'adi daya kacal. Saura sun hada da rabon mukaman siyasa a fadar shugaban kasa idan jam'iyyar mu ta ci zabe. Muna kyautata zaton za mu ci don haka gara mu tattauna rabon mukamai yanzu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

"Wani abu kuma shine cigaba da zaman a ofis na shugaban jam'iyyar mu, Iyorchia Ayu. Dan takarar shugaban kasar a baya-bayan nan ya ce zai sauka ne kawai idan ya ci zabe yayin da wasu cikin mu munyi imanin ba wannan bane yarjejeniyar da muka yi kafin gangamin Oktoban bara.
"Muna fatan za a warware dukkan wannan matsalolin yayin taron mu," kamar yadda aka rahoto majiyar na cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel