Ina Tare Da Wike, Ko Dazu Muna Landan: Ortom Ya Karyata Hadiminsa

Ina Tare Da Wike, Ko Dazu Muna Landan: Ortom Ya Karyata Hadiminsa

  • Gwamnan jihar Benue yace shi fa yana tare da Gwamnan Rivers Wike ba shugaban jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, ba
  • Mai magana da yawun Ortom da a ranar Litnin ganin kare maigidansa yace sun raba jiha da Wike
  • Rikicin jam'iyyar PDP ya ki ci, ya ki cinyewa yayinda ake shirin kaddamar da yakin neman zabe

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya karyata rahotannin cewa ya yi hannun riga da Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, kan rikicin da ya kara'de jam'iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP).

Dazu kun ji cewa Gwamnan Ortom, a ranar Litnin, ya yi watsi da rahotannin cewa yana goyon bayan tsige Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Atiku vs Wike: Gwamna Ortom Ya Raba Jiha Da Wike, Ya Ce Yana Tare Da Ayu

A jawabin da sakataren yada labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar a Abuja, Ortom yace kowa ya sani cewa su sukayi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa Ayu ya zama shugaban PDP.

Amma a martanin da yayi ranar Talata, Ortom ya karyata hadiminsa inda yace har yanzu bai sauya matsayarsa ba, rahoton DailyTrust.

Ortom
Ina Tare Da Wike, Ko Dazu Muna Landan: Ortom Ya Karyata Hadiminsa
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hira da manema labarai a Makurdi, Ortom yace ya zama wajibi ya fayyace gaskiyan inda ya tsaya.

Yace:

"Maganar cewa na raba jiha da Nyesom (Wike); dawowata daga Landan kenan tare da shi da safen nan (Talata). Abokina ne kuma ina kan baka na. Ban sauya ba. Ina tare da Wike bisa rashin adalcin da akayi masa."
"Shugabannin jam'iyya basu yiwa Wike adalci ba biyo bayan abubuwan da suka faru bayan taron gangamin."
"Har yanzu mun gaza sulhu tsakaninmu. Ina tare da shi kuma ina kira ga shugabannin uwar jam'iyyar su tsaya tare da shi.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel