Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

  • Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya yi martani ga tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido kan maganan da ya yi game da rikicinsu da Atiku Abubakar
  • Lamido, cikin hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Talata ya ce babu bukatar a yi wani sasanci da Wike domin babu wanda ya masa laifi
  • Wike a bangarensa ya ce Lamido bai da wani tasiri a jam'iyyar PDP, ya kuma ce shi da abokansa ne suka janyo jam'iyyar ta sha kaye a 2015

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

Sule Lamido
Wike: Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma, Wike cikin sanarwar da kakakinsa, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana kalaman da aka danganta da Lamido a matsayin abin kyama da raini.

Wani sashi na sanarwar:

"Watakila Alhaji Lamido yana tunanin yan Najeriya suna da ciwon mantuwa ne idan yana ganin sun manta da mummunan rawar da shi da abokansa suka taka daga 2014 zuwa 2015, da ya janyo shan kayen PDP a babban zaben 2015.
"Muna fatan ba abin da ya ke son sake maimaitawa ba kenan. Idan ba haka ba, Idan Alhaji Lamido ya san ya kamata, bai dace ya rika furta maganganu marasa kyau kan Wike ba, wanda mutane da dama suka kira madogara na PDP tun 2015."

Gwamna Wike, kamar yadda sanarwar ta ce ya kara da cewa yana fata Lamido zai mayar da hankali wurin ceto mutuncinsa ya kawo wa PDP Jihar Jigawa a zaben 2023 idan zai iya.

Kara karanta wannan

A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Gwamna Sule Lamido

2023: Wike Zai Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zabe Cikin Sauki, Masari

A wani rahoton, Alhaji Ibrahim Masari, na hannun daman ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana fatan da suke bayan ganawa da gwamnan Ribas Nyesom Wike a birnin Landan.

Vangaurd ta rahoto cewa Masari ya ce suna da kwarin guiwa bayan zaman Landan, gwamna Wike zai yi aiki tuƙuru domin nasarar Tinubu a babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel