Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan yadda sabbin shugabannin Najeriya za su samu a 2023
  • Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta gudanar da tsarin mika mulki mai cike da nagarta
  • Ya bukaci sabbin jakadun kasar da suka gabatar masa da wasikun kama aiki da su zamo masu karfafa alakar da magabatansu suka shimfida

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna yakinin cewa gwamnatinsa za ta gudanar da tsarin mika mulki mai kyau inda sabbin shugabannin siyasa zasu bayyana.

Shugaban kasar ya yi jawabi ne a ranar Talata yayin da ya karbi wasiku daga jakadu da manyan kwamishinonin kasashe shida a fadar shugaban kasa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Buhari
2023: Yadda Sabbin Shugabannin Najeriya Za Su Bayyana – Buhari Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jakadu da manyan kwanishinonin sun hada da na Indiya, Mista Gangadharan Balasubramanian, Jamus, Annett Gunther, Sudan, Mohamed Yousif Ibrahim Abdelmannan, Damocradiyar Kongo, Misis Gerengbo Yakivu Pascaline.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Atiku Zai Gana Da Wasu Ƙusoshin Jam'iyyar PDP Na Kudu Maso Gabas

Sai na Palestine, Abdullah M.A. Abu Shawesh da na masarautar Netherlands, Mista Willem Wouter Plomp, kuma duk sun gabatarwa Shugaba Buhari bda wasikun yardan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi, Buhari yace:

“Ina da yakinin cewa za mu gudanar da tsarin mika mulki mai nagarta wanda a karshensa sabbin shugabanni zasu bayyana.
“Zaku fara aikinku na jakadanci a Najeriya, a daidailokacin siyasa domin zaben Najeriya na zuwa a watan Fabrairun 2023. Ina so na kara nanatawa kamar yadda nayi a kwanakin da suka gabata a taron UN, cewa muna ci gaba da jajircewa don zabe na gaskiya.”

Shugaban kasar, wanda ya bayar da tabbacin cewa za a ci gaba da karfafa damokrdayya ta hanyar yancin magana da kuma fafutukar siyasa ya nemi da a mutunta al’adu da ra’ayoyi mabanbanta, tare da tabbatar da hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu

Buhari ya kuma bukaci jakadun da su ci gaba a kan kyakkyawar alakar da magabatansu suka gina ta yadda za su kara kaimi wajen gudanar da ayyuka, Arise News ta rahoto.

A madadin jakadun, babban kwamishinan Indiya a Najeriya ya baiwa shugaba Buhari tabbacin samun cikakken goyon bayan kasashensu, musamman ganin yadda Najeriya ke gab da shiga zaben 2023.

Ya kara da cewa za su yi aiki da gwamnatinsa, da kuma shugaban da zai fito bayan zaben.

An Gargadi Tinubu Kan Shirinsa Na Amfani da Kudi Wajen Raba Kawunan Kiristoci a Zaben 2023

A wani labarin, mun ji cewa an gargadi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan amfani da kudi wajen kawo rabuwar kai tsakanin Kiristoci.

Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kungiyar dattawan Kirista a jihohin arewa, dauke da sa hannun shugabanta, Oyinehi Inalegwu, a ranar Talata, 27 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel