Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya

Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya

  • Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara
  • Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni
  • Ɗan bindigan ya yi gargaɗin cewa a shirye yake ya bi duk abinda gwamnati ta zaɓa tsakanin zaman lafiya da yaƙi

Zamfara - Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, yace cin amana ne harin da Sojojin Najeriya suka kai sansaninsa a jihar Zamfara.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda wani luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya ya yi sanadin kashe gomman yan ta'adda a mafakar Turji.

Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin dajin sun halarci wurin ɗaura aure tare da Bello Turji lokacin da jirgin NAF ya yi ruwan bama-bamai a wani yankin ƙaramar hukumar Shinkafi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga tasku, sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a maboyar kasurgumin dan ta'adda

Belli Turji.
Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya Hoto: thecable
Asali: UGC

Sai dai an ce Turji ya tsallake rijiya da baya. A wani faifan Audio da jaridar PRNigeria ta samu, ƙasurgumin ɗan bindigan ya nuna ɓacin ransa kan harin jirgin duk da ya amince ya watsar da ayyukan ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bamu kai hari ba an samu zaman lafiya tsawon watanni biyar amma yanzu da Sojoji suka farmaki gidanmu, muna jin an ci amanar mu musamman ganin yadda muka rasa mutane a harin Jirgin yaƙi."
"Watanni 5 da suka shude bamu kai hari ko kashe mutun ɗaya ba a yankin Shinkafi. Sakamakon haka Noma da sauran harkokin kasuwanci sun fara farfaɗo wa ba tare da fargaba ba."
"Na ji kunya da aka ambaci sunana bayan wasu 'yan fashin daji da 'yan ta'adda sun kai hari. Bayan gidana da aka tasa aiki, mafi yawan gidajen mutanen da ba ruwansu a Jejin harin jirgin ya taɓa su."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Wani Katon Bene Ya Ruguje, Ana Kokarin Ceto Wadanda Ya Danne a Legas

- Bello Turji, a faifan maganar da ya fito.

A shirye muke mu rungumi zaman lafiya - Turji

Ɗan bindigan ya ƙara da cewa a shirye yake ya rungumi zaman lafiya mai ɗore wa matukar gwamnati ba so take ya sake ɗaukar makami ba.

"Zaman lafiya ya zarce darajar komai kuma a shirye nake na rungumi zaman lafiya matuƙar ba gwamnati na kokarin tunzura ni na koma fagen yaƙi ba. A shirya nake a zauna lafiya ko a yi yaƙi."
"Duk abinda gwamnati ta zaɓa a shirye muke mu ba su ninkinasa, zaman lafiya ko yaƙi."

Bello Turji ya tuɓa - Sanata Nasiha

Wannan cigaban ya faru ne ƙasa da wata ɗaya, bayan Sanata Hassan Nasiha, mataimakin gwamnan Zamfara yace Turji ya karɓi shirin zaman lafiya da gwamnati ta zo da shi.

Nasiha yace ƙasurgumin ɗan bindigan ya daina kai wa al'umma hari, ya koma kan 'yan ta'addan da suka ƙi amince wa su tubarwa Allah.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

A wani labarin kuma Bello Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsagin Bello Turji ya kaure da azababben faɗa da ɓangaren wani shugaban 'yan ta'adda, Ɗan Bokolo.

Wata majiya tace tawagar yan ta'addan biyu sun barke da yaƙi ne baya kai wasu hare-hare kauyuka a Shinkafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel