Da Duminsa: Wani Katon Bene Ya Ruguje, Ana Kokarin Ceto Wadanda Ya Danne a Legas

Da Duminsa: Wani Katon Bene Ya Ruguje, Ana Kokarin Ceto Wadanda Ya Danne a Legas

  • Wani katon bene ya sake rugujewa a titin Sonuga dake Palm Avenue a yankin Mushin dake Legas a Najeriya
  • Kamar yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa, Olufemi Oke ya sanar, lamarin ya faru ne a ranar Juma'a
  • A halin yanzu an tabbatar da cewa ana aikin ceto wadanda ginin ya danne duk da ba a tabbatar da yawansu ba

Legas - Wani katon gini ya ruguje a kan titin Sonuga, Palm Avenue, a anguwar Mushin dake jihar Legas.

Babban Sakatare na Hukumar bayar da agajin gaggawa na Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar wa da jaridar Punch da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Bene ya rushe
Da Duminsa: Wani Katon Bene Ya Ruguje, Ana Kokarin Ceto Wadanda Ya Danne a Legas. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Yace:

“Wani gini ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci kadan da suka gabata. Ana ci gaba da aikin ceto wadanda ibtila'in ya ritsa da su.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani bene ya ruguje a wata jihar Arewacin Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, ba a iya tabbatar da mutane nawa ne ke cikin ginin ba yayin da ruguje da kuma wadanda ya danne.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel