Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara

Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar gano mafakar 'yan bindigan da suka addabi jihohin Zamfara da Katsina a Arewacin Najeriya
  • Majiya ta ce, an hango hayaki a daidai lokacin da sojojin suka saki bama-bamai a sabon farmakin da suka kai a jiya Alhamis
  • 'Yan ta'adda a Arewacin Najeriya na shan ragargazar soja a 'yan kwanakin nan, an hallaka tsageru da dama

Zurmi, jihar Zamfara - Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sake gano mafakar 'yan ta'adda karkashin jagorancin Dan Karami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ce, sojojin sun yi nasarar jefa bama-bamai kan mafakar 'yan bindigan da ke addabar jama'ar yankin.

Yadda sojin sama suka ragargaji maboyar 'yan ta'adda a Zamfara
Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara | Hoto: saheliantimes.com
Asali: UGC

A cewar wata majiyoyi daga yankin, an kashe wasu 'yan bindiga da dama a harin da aka kai jiya Alhamis 22 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga dajin Sambisa, sun sheke 'yan Boko Haram 36, sun ceto mutane da yawa

Mun hango hayaki a ta inda mafakar 'yan ta'adda take, inji wani

Wani mazaunin yankin, Musa Shehu yace ya ga tashin hayaki daga nesa, wanda yace tabbas daga mafakar 'yan ta'addan ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Sojojin sama ne suka farmaki mafakarar da yammacin nan (Alhamis) kuma mun ga hayaki daga bangaren."

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a san ko Dan Karami na daga cikin 'yan ta'addan da suka mutu a farmakin na soja ba, inji Sahelian Times.

Dan Karami wani kasurgumin dan bindiga ne da ke jagorantar ayyukan ta'addanci kan mazauna jihohin Zamfara da Katsina a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sojojin Najeriya Sun Sheke ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 36, Sun Ceto Mutane 130 a Arewa Maso Gabas

A wani labarin, hedkwatar tsaro ta Najeriya ya ce dakarun tawagar Operation Hadin Kai ta yi nasarar kawar da 'yan ta'adda sama da 36 a ayyuka daban-daban ta sama a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni biyu.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun tarfa 'yan ta'addan Boko Haram, sun hallaka da yawa a jihar Borno

Daraktan yada labarai na ayyukan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a jawabin nasarorin da jami'an tsaro ke samu a yau Alhamis 22 ga watan Satumba a Abuja.

Danmadami ya kuma bayyana cewa, an hallaka kasurguman shugabannin 'yan ta'ddan ISWAP da Boko Haram; Abuja Asiya da Abu Ubaida a aikin, rahoton masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel