Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

  • Yan Najeriya su shirya, da alamun za'a sake shiga duhumun-buhuman cikin mako mai zuwa
  • Ma'aikatan kamfanonin lantarkin Najeriya sun ce har yanzu gwamnati bata cika alkawarinta ba
  • Daya daga cikin shugabannin kungiyar yace damfarar Najeriya akayi da sunan sayar da kamfanonin wa masu zuba jari

Kaduna - Kungiyar ma'aikatan lantarki a Najeriya watau National Union of Electricity Employees (NUEE) ta sake barazanar kashe wutar kasar gaba daya idan gwamnati ta ki biyan bukatunta.

Wannan ya biyo bayan karewar wa'adin makonni biyu da mambobin kungiyar suka baiwa gwamnati.

Lantarki
Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya
Asali: Facebook

Sakataren Shirye-Shirye na yankin Arewa maso yamma, Dukat Ayuba, a hira da manema labarai a Kaduna ranar Alhamis ya ce har yanzu sun tattaunawa amma zasu iya kashe wuta a koda yaushe, rahoton TheNation.

Ayuba ya laburta cewa lamarin sayar da kamfanonin lantarkin duk damfara ne saboda shekaru 9 bayan haka babu sauyin da aka samu.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: An kashe 'yan jiha ta 5000 cikin shekaru 11 a hare-haren 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Shi yasa muka ki yarda da sayar da kamfanonin raba lantarki, wadanda suka saya basu da karfi da ilimi. Mun baiwa gwamnati shawara amma ta ki."
"Har yanzu da tsaffin injinan sama da shekaru 35, 40 zuwa 50 ake amfani. Abinda aka yi tsammani shine masu zuba jarin da suka saya zasu zuba sabbin kayan aiki amma babu abinda suka yi."

Ya kara da cewa har yanzu megawatt 5000 na lantarki ake hakowa sama da shekaru 9, ton menene amfani sayar da kamfanin?

"Yanzu farashin lantarkin ya tashi. Hakan ya haifar da tsadar rayuwa ga miliyoyin yan Najeriya. Babu inda irin wannan abu zai faru illa Najeriya."

...Ya kara

Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina

Gwamnatin Tarayya a daren ranar Talata ta ce wutar lantarki ta inganta a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari matuka idan aka kwatanta da yadda ta ke a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV.

Adesina ya ce kwantiragin da gwamnatin tarayya ta yi da kamfain Siemens ne yasa ake kawo transifoma da wasu kayan lantarki don magance matsalar dauke wuta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel