Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu

Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu

  • Iyayen daliban da 'yan bindiga suka sace a kwalejin tarayya ta Birnin Yauri a Kebbi sun ce sun fitar da ran samun taimakon gwamnati
  • Iyayen sun bayyana alhininsu kan yadda 'ya'yansu suka kwashe kwanaki 87 hannun miyagu tun bayan da aka kutsa makarantar aka sace su
  • Duk da iyayen daliban sun ce da 'ya'yan gwamnati ne, ba za su kai yanzu ba, gwamnatin jihar ta ce ta na iyakar kokarin ta wurin karbo yaran

Kebbi - Iyayen daliban da aka sace na makarantar kwalejin tarayya da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi sun ce sun fitar da ran cewa gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu da aka sace.

A halin yanzu, daliban sun kwashe kwanaki 87 a hannun miyagun da suka sace su, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu
Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan bindiga kusan 150 sun kutsa makaranta a tsakar rana kuma sun yi awon gaba da dalibai sama da 90 tare da malaman makarantar.

Musa Sulaiman, mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace a makarantar, ya ce ya cire rai kan cewa gwamnatin Kebbi ko ta tarayya za ta iya karbo musu yaransu da aka sace kusan watanni 3 da suka gabata.

Ya jaddada cewa, gwamnatin jihar ba wannan ne karon farko da ta fara shirga alkawarin karya na fito musu da 'ya'yansu ba.

Sulaiman, wanda ya ce gwamnati ta nuna rashin damuwarta, ya jaddada cewa da yaransu ne aka sace, da tuni a halin yanzu sun dawo gida.

Ya ce:

"Gwamnati ta yi mana alkawari kusan sau hudu ko biyar kan cewa za ta karbo mana yaranmu, amma har yanzu ba ta cika ba

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

"Mun fitar da rai gaskiya. Idan ba don 'yan bindigan suna cewa sai da gwamnati za su yi ciniki ba, da tuni mun yi amfani da 'yan kudin da muka mallaka mun karbo yaranmu,"

Wasiu Abdulraheem, wanda diyar shi daya tilo da ya ke da ita aka sace, ya ce ya shirya yin komai wurin ceton diyar shi. Ya ce tun bayan sace diyar shi ya fada cikin mawuyacin hali.

Abdulraheem, wanda ya zanta da Daily Trust cikin kunar rai da kunci, ya ce tun bayan sace diyar shi ya ke fama da cutar hawan jini. Ya yi kira ga jama'a da su taimaka wurin ceton 'ya'yansu.

A yayin da aka tuntubi mai bada shawara na musamman ga gwamna kan lamurran tsaro, Kanal Rabiu Garba Kamba, ya ce gwamnati ta na kan matsalar kuma ba za ta sassauta ba wurin tabbatar da cewa daliban da aka sace an sako su.

Kara karanta wannan

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa

A wani labari na daban, rufe kasuwanni masu yawa a fadin jihohin arewa maso yamma na Najeriya ya kasance babban kalubale ga 'yan fashin daji.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kalla gwamnonin yankin hudu ne suka umarci rufe kasuwannin jihohinsu a matsayin hanyar dakile ta'addanci.

Kwanaki kadan bayan rufe kasuwannin a wasu kayukan Sokoto, 'yan fashin daji sun fara bukatar kayan abinci a matsayin fansar wadanda ke hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel