Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya yi magana a kan shirin duba albashin ma’aikata
  • Dr. Chris Ngige yace hauhawan farashin kaya ya lamushe karin albashin da gwamnati tayi a 2019
  • Dokar albashi ta bada damar a duba abin da ma’aikata suke karba, domin ya dace da tsadar rayuwa

Abuja - Gwamnatin taryya ta bayyana cewa akwai shirin kara mafi karancin albashi daga N30, 000 da akalla kowane ma’aikaci ya kamata ya karba.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dr. Chris Ngige, ya dauko wannan magana da yake jawabi a garin Abuja.

Chris Ngige ya gabatar da wata takarda a kan gwagwarmayar ma’aikata a kasar nan, inda ya nuna cewa ana fama da hauhawar farashin kaya a Duniya.

Ministan yace tsadar da kaya suka yi a ko ina, ya jawo darajar kudi ya ragu sosai, wannan ya sa gwamnati take la’akari da batun sake yin karin albashi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Kowa na kuka a Duniya

“Hauhawar farashi ya shafi duk Duniya, za mu daidaita mafi karancin albashinmu daidai da yadda abubuwa suke.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne, a dokar albashi ta shekarar 2019, akwai sashe da ya bada damar a rika duba albashin.”

- Dr. Chris Ngige

Chris Ngige
Sanata Chris Ngige Hoto: nnn.ng
Asali: UGC

Halin da malaman Jami'a ke ciki

Punch ta rahoto Ministan yana cewa an fara maganar kara albashin da ‘yan kungiyar ASUU, ana kokarin kara abin da malaman jami’a ke karba.

A game da batun malaman jami’an da ke ta yajin-aiki, Ngige ya nuna akwai yiwuwar a cigaba da hana su albashi domin ba suyi aiki, sun rufe makaranta.

An rahoto Ngige yana cewa gwamnati na shirin maida cibiyar nazarin ilmin kwadago ta Michael Imoudu ta zama makarantar da ake samun Digiri.

Adams Oshiomhole ya yi magana

Kara karanta wannan

An Jefar da Karar da Abduljabbar Kabara Ya Kai Gwamnati, An Ci Shi Tarar N100, 000

Jawabin Ministan ya zo ne bayan shugaban kungiyar TUC na kasa, Festus Osifo ya yi magana a kan yadda mala’u suke murkushe ma’aikata a Najeriya.

A rahoton The Nation, an ji Adams Oshiomhole wanda ya taba rike kungiyar NLC, yana bada shawara ga shugabannin kwadago game da zaben 2023.

Adams Oshiomhole yace ya kamata NLC ta rika bin manufofin ‘yan takarar shugaban kasa, sannan ya yi tir da gwamnonin da har yau ba su biyan N30, 000.

An ci Shehi tara a kotu

A ranar Litinin aka ji labari cewa Kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yi zama domin sauraron karar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnatin Kano.

A karshen zaman da aka yi, kotu ta bukaci Lauyan da ya tsayawa malamin ya biya tarar N100, 000 ga gwamnati saboda ya nemi ya raina hankalin shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel