Yadda Dan China Ya Shiga Har Gida Ya Yiwa Diyata Kisan Gilla, Mahaifyar Ummita

Yadda Dan China Ya Shiga Har Gida Ya Yiwa Diyata Kisan Gilla, Mahaifyar Ummita

  • Mahaifiyar Ummita, wata matashiyar da aka kashe a jihar Kano ta bayyana yadda lamarin ya faru tun farko
  • Ta ce, Ummita ta yiwa dan China alkawarin aure, amma hakan bai yiwu ba har daga baya budurwar ta yi aurenta
  • Ya zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin dan Chinan ba da kuma dalilinsa na daukar doka mai tsauri haka a hannunsa

Jihar Kano - Wani rahoton Daily Trust ya ce, mahaifiyar Ummukulsum Sani Buhari, matashi mai shekaru 23 da wani dan China ya kashe a jihar Kano ta yi bayanin yadda lamarin ya faru.

Idan baku manta ba, a jiya ne Juma'a 16 ga watan Satumba wani tsageran dan China ya shiga har gida ya hallaka wata matashiya a Janbulo ta karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Yadda dan China ya kashe matashiya a jihar Kano
Yadda dan China ya shiga har gida ya yiwa diyata kisan gilla, mahaifyar Ummita | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matashiya wacce aka fi sani da Ummita ta yi karatun unguzoma a makarantar Kano School of Nursing and Midwifery.

Bayan binne da karfe 10 na safiyar Asabar, batutuwa sun fito daga bakin mahaifiyarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faru

Jaridar Daily Trust ta naqalto mahaifiyar na cewa:

“Diyata ce; shi (dan Chinan) yakan zo gida kullum yana neman ganinta kuma ta sha kin fitowa. A wannan karon da ya zo, ya ta buga kofa. Da na gaji da bugun kofarsa da karfi, na bude kawai sai ya ture ni gefe ya shiga gidan ya fara caccaka mata wuka.
"Na fara ihu daga nan mutane suka fara shigowa a guje. Muka dauke da nufin kaita asibiti amma kafin mu isa, ta rasu. Hakan ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare.
"Muna gida a lokacin tare da kannenta mata biyu. Yayanta baya nan ya fita mahaifinta kuma ya rasu. A lokaicn ana ruwa, kowa na cikin gida kuma ba kowa ne ya ji ihu na ba haka dai wani yaji sai ya faso ta taga ya shigo.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

"Ina son hukumomi su duba wannan aikin ta'addancin. Tuni dama batun soyayyarsu ta kare. Ta yi aure amma daga baya aka sako ta. Daga nan ne ya yi kokarin dole sai ya ganta.

Dan Chinan na shiga har gida, ya san dakin Ummita, inji mahaifiyarsa

Da take bayyana alakarsa da diyarta, mahaifiyar Ummita ta ce tabbas ta masa alkawarin aure, kuma yakan zo har gida duk da cewa ba da sonta bane.

Ta kara da cewa:

"Yakan shiga har gida duk da cewa bamu son hakan amma ya gaza fahimta. Mukan kore shi. Da na yi yunkurin sanar da 'yan sanda, 'ya'yana sun ki hakan suka ce bai kamata batun ya fita waje ba.
"Mutumin da ya shigo ya shigo ne ta taga, shi ne ya kama shi ya fitar dashi. Ya guda, aka bi shi aka kama shi aka dawo dashi. A yanzu yana hannun 'yan sanda. Ita ce babbar diyata mace amma tana yayu maza biyu.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

"Ya san bata son ganisa. Idan ya kira bata dauka. Wannan yasa ya yanke shawarar kutsawa cikin gida. Ya buga kofa na kusan awa hudu. Ita ta tura ni na kore shi daga nan ne ya ture ni a lokacin da bude kofa
"Ya tafi kai tsaye zuwa dakinta. Yasan inda dakin yake saboda yakan zo. A wasu lokutan, yayanta ne ke korarsa. Sun fara haduwa ne a Shoprite a lokacin da ta je siyan turare a nan ne suka samu lambar juna. Daga nan ne suka fara waya.
"A lokacin da ta yi aurem sun rabu har bayan da aka sake ta. Mijinta ya zargi suna waya da dan Chinan duk da cewa ba hakan ne silar mutuwar aurenta ba. Tabbas, ta ce za ta aure shi, amma da kawunta ya hango wasu matsaloli a gaba, sai ya ki nima na goyi bayan hakan."

'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Kara karanta wannan

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Fitaccen Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

A wani labarin, wani mutun 'dan kasar China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta mutu a take a kwatas din Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan wanda ake zargin ya kai wa budurwa mai suna UmmaKulsum Sani Buhari ziyara a gidan iyayenta dake kusa da ofishin National Environmental Standards and Regulations Enforcement Agency (NESREA).

Yayin da abinda ya hada masoyan biyu har yanzu ba a gano shi ba, Daily Trust ta tattaro cewa likitoci sun tabbatar da mutuwar budurwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel