Sojoji Sun Tarwatsa Boko Haram Za Suyi Sallar Gawa, Sun Sake Kashe Na Kashewa

Sojoji Sun Tarwatsa Boko Haram Za Suyi Sallar Gawa, Sun Sake Kashe Na Kashewa

  • Adadin mayakan Boko Haram da suka mutu a ‘yan kwanakin nan a garuruwan Borno sun haura mutum 200
  • Wasu sun mutu a sakamakon harbin bindiga, jirgin yaki ya kashe wasu, wasunsu kuma sun nutse a cikin ruwa
  • ‘Yan ta’addan sun dauko gawawwaki domin suyi sallah, sai jirgin Super Tucano ya sake yi masu luguden wuta

Borno - Mayakan Boko Haram da-dama sun bakunci barzahu a wasu danyun hari da dakarun sojojin kasar Najeriya suka kai masu a karshen makon jiya.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba 2022, wanda ya nuna an hallaka ‘yan Boko Haram a hare-hare da sojoji suka kai masu.

‘Yan ta’addan sun mutu bayan luguden wuta daga jiragen sojojin sama da kuma rundunar sojojin kasa a wasu artabu da aka yi cikin 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun kai Sabon Farmaki Abuja, Sun Tafka Mummunar Ta'asa

Boko Haram sun yi asarar sojoji kimanin 200 da manyan jagororinsu biyar.

Boko Haram za su yi wa gawa sallah

Bayan luguden wuta da sojoji suka yi wa ‘yan ta’addan a Mantari, Mallum Masari da Gaizuwa, rundunar jami’an tsaro sun hallaka masu shirin jana’iza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace a ranar Asabar, an hallaka wasu ragowar ‘yan ta’addan yayin da suka zo daukar gawar mayakansu da aka hallaka a Sheruri da Gabchari.

Tucano
Jirgin Super Tucano Hoto: humanglemedia.com
Asali: UGC

An samu gawawwakin ‘yan ta’addan na Boko Haram wadanda suka nutse a ruwa a Gabchari.

An kuma samu gawawwakin akalla mutane 9 da suka mutu a sakamakon harbin bindiga. Daga ciki har da manyan jagorori Abou Zainab da Abou Idris.

Jirgin Super Tucano

Majiyar tace yayin da ‘yan ta’addan ke kokarin yi wa mamatansu sallar gawa, sai sojoji suka samu labari, nan da nan suka fara shawagi da Super Tucano.

Kara karanta wannan

Yadda Ake Hada Kai da Jami’an tsaro da Jami’an Gwamnati, Ana Sace Man Najeriya

Kafin ‘yan ta’addan su farga, sai jirgin Super Tucano yayi musu ruwan wuta.

Ana kyautata zaton da-dama daga cikin mayakansu sun mutu a sanadiyyar barin wuta daga sama.

Biyo bayan hakan ne yan ta'addan na Boko Haram da suka rage suka shiga fagamniya, suka boye a bishiya domin su tsira da ransu, daga baya wasu sun arce.

Zuwa yanzu ba a san adadin wadanda aka harbe a cikin wadanda aka tarwatsa za su yi sallar ba.

Abba Kyari ya shiga uku

Dazu kun ji labari Gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigar da sabon kara a kan Abba Kyari, ‘Yanuwansa biyu da mataimakinsa a IRT, ACP Sunday Ubua

Bincike ya nuna DCP Abba Kyari yana da gidaje, gidan gona da shaguna a Abuja, sannan yana da kadarori da filin wasan folo, duk ba a san da zaman su ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haream 200 Da Manyan Kwamandoji 5

Asali: Legit.ng

Online view pixel