'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Abuja, Sun Kashe Mutane Sun Sace Manoma

'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Abuja, Sun Kashe Mutane Sun Sace Manoma

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da manoma 13 a yankin babban birnin tarayya Abuja
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kutsa har cikin gida suka sace mutane a ƙauyen Rafin Daji, daga bisani suka wuce Kutara
  • Kakakin hukumar yan sanda bata amsa sakonnin karta kwanan da aka aike mata game da sabon harin ba

Abuja - 'Yan bindiga sun ci karensu babu babbaka ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:00 na dare a kauyukan Rafin Daji da Kutara dake gundumar Gurdi, ƙaramar hukumar Abaji, birnin Abuja.

Yayin wannan sabon farmakin, 'yan ta'addan sun kashe mazauna ƙauye biyu, sannan suka yi awon gaba da wasu manoma 13.

Harin 'yan bindiga a Abuja.
'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Harin Abuja, Sun Kashe Mutane Sun Sace Manoma Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwanaki Tara da suka gabata, 'yan bindiga sun kai farmaki ƙauyukan Gasakpa da Mawogi dake gundumar Gawu, duk a ƙaramar hukumar Abaji, inda suka yi garkuwa da manoma Takwas.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Wani ɗan uwan mutanen da harin ranar Asabar ya shafa a Rafin Daji, Shu'aibu Ɗantani, yace yan bindiga sun tafka ta'asarsu babu tirjiya, suka buɗe wuta don tsorata mutane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, maharan sun kutsa cikin gidaje huɗu, suka tattara manoman suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da babu wanda ya sani.

Bugu da ƙari, Ɗantani yace yan bindigan sun zarce zuwa ƙauyen Kutara dake makwaftaka da su, suka hallaka mutum biyu, daga bisani suka ɗauki miji da mata a ɗakin kwanansu.

Magajin garin Gulida a gundumar Gurdi, Sadauna Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar salula.

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta maida sakon karta kwanan da aka tura mata game da sabon harin garkuwa da mutanen ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Yan sanda sun gwabza da yan fashin daji a Katsina

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannun Yan Sanda Yayin da Suka Yi Yunkurin Sace Dan Takarar PDP

Gwaraazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262