An Bankado Wasu Dukiyoyin Abba Kyari, An Sake Kai Shi Kotu da Zargin Laifuffuka 24

An Bankado Wasu Dukiyoyin Abba Kyari, An Sake Kai Shi Kotu da Zargin Laifuffuka 24

  • Gwamnatin Tarayya tana zargin Abba Kyari yana da wasu gidaje, shaguna da kadarori da ba a san da su ba
  • Bincike ya nuna akwai rukunin gidaje da shaguna da gidan gona da DCP Abba Kyari ya mallaka a birnin Abuja
  • Ana kuma tunanin Kyari yana da wurin wasan folo da wasu dukiyoyi a Borno, ban da tulin kudi na kasar waje

Abuja - Gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka. Tun tuni dai ake shari’a da babban jami’in ‘dan sandan.

Punch ta fitar da rahoto cewa binciken gwamnatin Najeriya ya gano akwai katafaren shaguna, rukunin gidaje da wani filin folo da Abba Kyari ya mallaka.

Haka zalika an gano wasu filaye da gidaje a hannun tsohon shugaban na dakarn IRT na kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Rahoton yace DCP Kyari bai fadawa hukuma cewa yana da wadannan kadarori a babban birnin tarayya Abuja da garin Maiduguri a jihar Borno ba.

Baya ga haka, an samu fiye da Naira miliyan 207 da fam Є17,598 a wasu asusun bankinsa. Darajar wadannan kudi na kasashen waje ya kai N10m.

Magana ta je kotu

Wannan ya sa Darektan shari’a da gurfanarwa, J. Sunday ya shigar da karar Abba Kyari a kotu a madadin gwamnati, ana tuhumarsa da laifuffuka 24.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abba Kyari
Abba Kyari ana bakin aiki Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya yana zargin DCP Kyari da laifin boye gaskiya a game da mallakar wadannan dukiyoyi.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22 a kotun tarayya na garin Abuja. Mohammed Kyari da Ali Kyari suna cikin wadanda za su amsa laifi.

Lambar ACP Sunday Ubua ta fito

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotu ta wanke tsohon gwamnan Arewa daga zargin karkatar da N6.3bn

Baya ga shahararren ‘dan sandan da kuma ‘yanuwansa, gwamnati tana karar ACP Sunday Ubua wanda ya taba zama mataimakin DCP Abba Kyari a IRT.

Shi ma ACP Sunday Ubua zai amsa zargin aikata laifuffuka 24 a wata shari’ar dabam a kotu. Premium Times ta tabbatar da wannan labari a safiyar Litinin.

Kadarorin Kyari a Abuja, Borno

Jaridar tace ana zargin Kyari ya mallaki gida a Blue Fountain Estate a Karsana da shago a Guzape, da wasu rukunin gidaje a Asokoro, duk a birnin Abuja.

Baya ga haka ana tuhumar ‘dan sandan da kin sanar da cewa yana da filaye da filin hawan folo a Borno. Ba mu san yaushe za a fara sauraron shari'ar ba.

A watan Maris ne kuka ji labari Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan kasa ya rasu.

Marigayi DIG Egbunike ne jami’in da IGP ya ba alhakin gudanar da bincike a kan DCP Abba Kyari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel