Jami’ar Jihar Kaduna da Wasu da Suka Janye Daga Yajin Aikin ASUU

Jami’ar Jihar Kaduna da Wasu da Suka Janye Daga Yajin Aikin ASUU

Yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya shiga kwanaki 191 ya zuwa ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, sai dai, wasu jami’o’in jiha sun fice daga wannan hayaniya.

Jami’o’in da suka fice daga yajin, a cewar jaridar Punch su ne:

Jami'o'i sun hakura, wasu sun janye yajin aiki
Jami’ar Jihar Kaduna da Wasu da Suka Janye Daga Yajin Aikin ASUU | Hoto: LASUOfficial
Asali: Twitter

Jami'ar Jiha ta Kwara

  • Jami’ar Jiha ta Legas
  • Jami’ar Jiha ta Osun
  • Jami’ar Jiha ta Kaduna, da dai sauransu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, wasu jami’o’in jiha a Najeriya har yanzu suna cikin yajin, amma wasu tuni sun fara sanar da ranar kowama karatu.

Jami'ar Jiha ta Ekiti

Hukumomin Jami’ar Jiha ta Ekiti a ranar Laraba, 24 ga watan Agusta, ta umurci duk sabbin daliban shekarar 2021/2022 da su dawo makaranta a ranar Litinin domin tantance su, su yi rajista kana a wayar musu da kai.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar Malaman Jami’o’i Su Shiga Yajin-Aikin Da Babu Ranar Dawowa

Ladoke Akintola University of Technology (LAUTECH)

Bata sauya zane ba, kwanan nan ne hukumomun Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso a jihar Oyo suka nemi a dawo aiki, hakan na nuni da janye yajin aikin ASUU a jami'ar.

Magatakarda jami'an Dr Kayode Ogunleye, ne ya fitar da sanarwar a ranar 18 ga watan Agusta.

Sai dai, rahoton Leadership ya ce, mambobin ASUU a jami'ar sun tubure, sun ki dawowa bakin aiki.

Jami'o'in da suka ki dawowa aiki

Mafi yawan jami’o’in gwamnatin jiha na cikin yajin aikin tsundum saboda kungiyoyin ASUU a cikinsu sun ki komawa karatu saboda gazawar gwamnati

  • Jami'ar Jiha ta Gombe
  • Jami'ar Olabisi Onabanjo
  • Jami'ar Ilimi ta Tai-Solarin a jihar Ogun
  • Jami'ar Adekunle Ajasin ta jihar Ondo
  • Jami'ar Jiha ta Bauchi
  • Jami'ar Jiha ta Benue
  • Jamu'ar Ibrahim Babaginda a jihar Neja
  • Jami'ar Yusuf Maitama Sule a Kano
  • Jami'ar Jiha ta Imo
  • Jami'ar Jiha ta Nasarawa
  • Jami'ar Jiha ta Abia
  • Jami’ar Fasaha ta jihar Kano
  • Jami'ar Jiha ta Kebbi
  • Jami'ar Jaha ta Sokoto da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Sai an gyara: Shugaba a PDP Ya Yarda Akwai Zalunci a Jam’iyya a Rabon Kujeru

Babu Abin da Malaman Jami’a Ke Tsinanawa a Jami’o’i, Don Haka Su Koma Aiki, Inji Farfesa Maqari

A wani labarin, Farfesa Ibrahim Maqari, limami a babban masallacin kasa da ke Abuja ya tona asirin malaman jami'a da irin kurarin da suke na binciken karya.

Farfesa Maqari ya ce, babu wani bincike da malaman jami'a ke yi, kawai suna shantakewa ne su koya wa dalibai abin da suke koyarwa sama da shekaru 20 da suka sani.

Wannan magana na Farfesa na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'a a Najeriya ke yajin aiki saboda rashin samun yadda suke so daga gwamnatin Najeriya na jin dadin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel