Sai an gyara: Shugaba a PDP Ya Yarda Akwai Zalunci a Jam’iyya a Rabon Kujeru

Sai an gyara: Shugaba a PDP Ya Yarda Akwai Zalunci a Jam’iyya a Rabon Kujeru

  • Sanata Walid Jibrin ya fitar da jawabi a game da kokarin da aka yi na kawo karshen rigimar cikin gidan da ta kunno kai a jam’iyyar PDP
  • Walid Jibrin wanda shi ne Shugaban majalisar amintattu, yana da ra’ayin cewa mutanen Arewa sun karbe duk manyan mukaman jam’iyya
  • Atiku Abubakar ne ‘dan takaran shugaban kasa, sannan shugabancin jam’iyyar PDP da majalisar BoT suna hannun mutanen yankin Arewa

Abuja - Shugaban majalisar BoT na jam’iyyar PDP, Walid Jibrin ya hakikance a kan cewa babu adalci a jam’iyyarsu idan aka yi la’akari da mukamai.

A ranar Talata, 23 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto Sanata Walid Jibrin yana mai cewa ‘Yan Arewa ke rike da manyan mukamai da takara.

A wani jawabi da ya fitar, Walid Jibrin yace ba za ta yiwu shugaban jam’iyyar, shugaban BoT da ‘dan takara duka su fito daga yankin Arewa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Yarbawa Ya Yi Fatali da Tinubu, Ya Ayyana ‘Dan Takararsu na 2023

Tsohon ‘dan siyasar yake cewa PDP tana tafiya da kowa, kuma jam’iyya ce mai farin jini ta mutanen kasa ba wai ta wani bangaren ‘Yan Najeriya ba.

A cewar Jibrin, da su aka kafa jam’iyyar tun a shekarar 1998, kuma ba zai taba sauya-sheka ba, ya kuma fadi irin kokarin da ake yi na dinke baraka.

Dole a fadi gaskiya - Jibrin

“A matsayin shugaban BoT, dole in fadi gaskiya komai sukar da za ayi. Ba na jin tsoron kowa sai Ubangiji, da kuma manufar jam’iyyarmu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan PDP
Atiku Abubakar da Shugabannin PDP na kasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
Zan kara da cewa ni cikakken ‘dan PDP ne wanda ke zama da kafafunsa tun da aka kafa ta a 1998.”
“Ba zan bar PDP ba har in mutu, ina nan a kan cewa BoT ta na sauraron rahoton kwamitin sulhun da Gwamnan Adamawa da Farfesa Jerry Gana ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Ana Tsakiyar Rikici a PDP, Atiku Zai Kafa Kwamitin Da Za Su Yi Masa Yakin Zabe

Bayan nan BoT za ta duba shi da kyau, sai ta sanar da jama’a abin da ya kamata. Iyakarta kenan.”

- Walid Jibrin

PDP na so ta lashe zaben 2023

Kamar yadda aka rahoto a Premium Times kafin yanzu, Sanata Jibrin yace ana cigaba da sulhu a PDP, yace burinsu ayi nasara a zabe mai zuwa.

“Ina bada shawara mu maida hankali da kyau a kan yadda za mu lashe duka kujerun zabe a 2023.”

- Walid Jibrin

Wike zai tsallaka APC?

An ji labari ko da Jibrin yake wannan magana, Gwamna Nyesom Wike da mutanensa suna Turai, suna ganawa da ‘dan takaran APC a 2023, Bola Tinubu.

Gwamna Samuel Ortom da Gwamna Seyi Makinde suka wakilci bangaren Gwamna Nyesom Wike. Sai Kayode Fayemi da Babajide Sanwo-Olu suna tsagin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel