Babu Abin da Malaman Jami’a Ke Tsinanawa a Jami’o’i, Don Haka Su Koma Aiki, Inji Farfesa Maqari

Babu Abin da Malaman Jami’a Ke Tsinanawa a Jami’o’i, Don Haka Su Koma Aiki, Inji Farfesa Maqari

  • Limamin babban masallacin kasa da ke Abuja ya bayyana kadan daga yadda aikin jami'a yake, ya caccaki lakcarori
  • Ya yi tsokaci game da yadda malaman jami'a ke ganin kansu a matsayin wadanda ke bincike, alhali ba sa komai
  • Maganar Maqari na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar malaman jami'a ASUU ke tsaka da yajin aiki

FCT, Abuja - Farfesa Ibrahim Maqari, limami a babban masallacin kasa da ke Abuja ya tona asirin malaman jami'a da irin kurarin da suke na binciken karya.

Farfesa Maqari ya ce, babu wani bincike da malaman jami'a ke yi, kawai suna shantakewa ne su koya wa dalibai abin da suke koyarwa sama da shekaru 20 da suka sani.

Wannan magana na Farfesa na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'a a Najeriya ke yajin aiki saboda rashin samun yadda suke so daga gwamnatin Najeriya na jin dadin aiki.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

Farfesa Maqari ya kunto kura, ya ce malaman jami'a ba sa aikin komai
Babu wani binciken da malaman jami'a ke yi, kawai kwafi-kwafi suke, inji Farfesa Maqari | coverghana.com.gh
Asali: UGC

Sai dai, malamin ya bude wasu abubuwa game da malaman jami'a, inda ya ce aikin da suke bai taka kara ya karya ba, don haka su daina daga ma jama'ar kasa hankali kawai su ci gaba da aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma yi misali da karan kansa a lokacin da yake karantarwa a jami'a, inda yace ya taba shafe shekaru uku yana karantarwar awanni hudu kacal a kowane mako.

A kalaman malamin:

"Aikin nan da ake ta rigingimu a kai wai meye muke yi ne? Ina binciken da ake yi? Me ake yi? Ba fa a yi, karyace. Kwafan ayyukan wasu ake yi.
"Aikin awa hudu, biyar ko shida a sati, ni misali, za a ci wai kana bincike, duk fadi ne kawai ba a yi, Wasu watakila suna yi, 'yan tsiraru, amma 80% bisa 100% ba a yi.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaron Lafiyarsa

"Idan kaga mutum yana bincike to neman karin girma yake, sai ya dan tattara, kila ma ayyukan dalibansa ne a dan gyara a hada takardar bincike ko kuma su bashi ya sa sunansa ya buga a matsayin nasa ne don ya sami karin girma. Da zarar ya samu karin girma, alkalaminsa ya bushe."

Cece-kuce daga jama'a kan matun Maqari

Kalaman Farfesa Maqari sun tada kura kafafen sanda zumunta, lamarin da ya kai ga wasu ke ganin ya yiwa malaman jami'a kudin goro.

Sai dai, wasu da dama na da ra'ayin cewa, da gaske wasu daga cikin malaman jami'ar ba sa aiki ko tabuka komai a bincike, kawai suna bin gado ne su kwanta wasu su tiki aikin bincike.

A nasa martanin ga kalaman jama'a. Farfesa Maqari ya yi karin haske, inda ya bayyana manufofin maganganun nasa.

A wani rubutu da ya yada a Twitter kuma waikilin Legit.ng Hausa ya samu, ya bayyana makasudin yin wadannan maganganu, inda yace sakwannin da yake son isarwa a bidiyon su ne kamar haka:

Kara karanta wannan

Na Bar Koyarwa Har Abada Idan Aka Hana Mu Albashin Watanni 6 Inji Malamin Jami’a

"Kira ga hukuma ta kara inganta ryuwar malaman jami'a. Kira ga masu samar da doka su nemo hanyar da zasu samar da dokar da za ta tilasta jami'an gwamnati sanya 'ya'yansu a makarantun gwamnati. Kira ga malaman jami'a da su koma aikinsu kuma su ingantashi har ya jawo hankalin masu gujewa.
"Mai yuyuwa mu haduda daukacin malaman jami'a a 2/3. Sabanimu kia kawai a sashin 1/3 ne, inda mai yuyuwa na yi kuskure wajen bada nisbar nagartattun aiyukan bincike a jami'o'i da kuma rashin dacewar lokacin lura da halin da malaman ke ciki."

Sheikh Ibrahim Maqari ya yi Magana Game da Labarin 'zama' Limamin Masallacin Ka'aba

A wani labarin, Ibrahim Ahmed Maqari ya yi magana a kan jita-jitar da ta rika yawo daga ranar Lahadi, 21 ga watan Agusta 2022, na cewa an ba shi limancin harami.

Legit.ng Hausa ta fahimci Farfesa Ibrahim Ahmed Maqari ya maida martani ne a shafinsa na Twitter watau @ProfMaqari, ya nuna labarin nan ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Sheikh Ibrahim Maqari ya yi Magana Game da Labarin 'zama' Limamin Masallacin Ka'aba

Tun da aka wayi a gari a jiya, Shehin malamin yace an yi ta kiransa a wayar salula a game da wannan labari da ya karada shafukan sada zumunta na zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel