Akwai Yiwuwar Malaman Jami’o’i Su Shiga Yajin-Aikin Da Babu Ranar Dawowa

Akwai Yiwuwar Malaman Jami’o’i Su Shiga Yajin-Aikin Da Babu Ranar Dawowa

  • ‘Ya ‘yan kungiyar ASUU na reshen jami’o’i sun yi taronsu na musamman domin su duba matsayar yajin-aikin da su ke yi a Najeriya
  • Jami’o’i da-dama sun gamsu a zarce da yajin-aiki har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta biyawa ASUU jerin bukatun da ta gabatar
  • Idan haka ta tabbata, babu ranar bude makarantu domin malaman jami’a ba za su koma aiki ba duk da barazanar hana su albashinsu

Kaduna - Kungiyar ASUU ta reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta zabi a cigaba da yajin-aikin da ake yi har sai an biyawa malamai bukatunsu.

Rahoton da muka samu daga Dateline ya tabbatar da cewa mafi yawan ‘ya ‘yan kungiyar ASUU ta jami’ar sun gamsu cewa yajin-aikin da ake yi ya zarce.

Legit.ng Hausa ta fahimci a ranar Talata malaman jami’an suka yi zama a dakin taro na Abdullahi Smith da ke tsangayar fasahar jami’ar a Samarun Zariya.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Shugaban ASUU na reshen jami’ar, Farfesa Haruna Jibril ya nuna suna tare da ASUU NEC.

A zarce da yajin-aiki sai 2023

Jaridar tace taron ya yi zafi har wasu sun bada shawarar a daina tattaunawa da gwamnati, ta yadda za a cigaba da yajin-aikin har sai an canza gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake karanto matsayar kungiyar, Farfesa Haruna Jibril yace sun gamsu a dakatar da salon yajin-aikin da ake yi, ASUU ta shiga yajin-aikin sai baba-ta-gani.

ABU Zaria
Kofar Jami'ar ABU Zaria Hoto: www.theabusites.com
Asali: UGC

Har ila yau, kungiyar ta yi tir da yadda gwamnatin tarayya ta ke amfani da salo na bata mata suna, yace ASUU na gwagwarmaya ne domin ceto ilmin jami’a.

Matsayin ASUU a sauran Jami'o'i

Wannan ne matsayar reshen jami'ar Bayero da ke Kano, shugabannin kungiyar sun tabbatar da cewa ba su ja da baya wajen ganin an biya masu bukatunsu ba.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Majiyarmu ta shaida mana cewa irin wannan matsaya aka cin ma a karshen taron kungiyar ASUU na reshen jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Haka abin yake a jami’ar tarayya ta Lokoja a jihar Kogi da Jami’ar Modibbo Adama a Yola.

Idan labarin da muka samu daga wani malamin jami’a a Najeriya ya tabbata, ‘yan kungiyar ASUU na reshen UDUS sun zabi yajin-aikin ya zarce har 2023.

Sauran jami’o’in gwamnatin tarayya kamar UNN da ke Nsukka, Jami’ar Zik a Anambra da jami’ar tarayya ta Dutsinma ba su goyon bayan a komai aiki.

INEC tace babu murdiya a 2023

An samu rahoto INEC ta tabbatarwa ‘Yan Najeriya cewa su sha kuruminsu domin babu yadda za ayi magudi a zaben 2023 saboda an fito da na’urorin BVAS

Kwamitin NPC da cibiyar nan ta The Kukah Centre sun shirya taro idan aka tattauna a game da gudumuwar na'urar BVAS wajen yakar magudin zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

Asali: Legit.ng

Online view pixel