Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

  • Bidiyon wata zukekiyar amarya da angonta sun bayyana a shafukan soshiyal midiya, inda mutane suka tofa albarkacin bakunansu
  • An dai gano amaryar sanye da hadaddiyar doguwar riga irin na zamani tana tikar rawa yayin da komai ya ji zam a jikinta
  • Jama'a da suka ga bidiyon sun yiwa ma'auratan fatan alkhairi yayin da ake ma mijin addu'a kan Allah ya bashi ikon sauke hakkokin da suka hau kansa

Jama’a sun yamutsa gashin baki bayan bayyanar bidiyon wata zukekiyar amarya da angonta a wajen liyafar bikinsu.

Tuni dai jama’a suka nadawa wannan amarya kambun ‘amaryar mako’ domin dai komai ya ji zam a bangarenta.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an gano amaryar sanye da doguwar riga irin ta zamani yayinda angonta ya sanya farar shadda dinkin babban riga.

Kara karanta wannan

Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya

Amarya da ango
Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Amarya Da Angonta Ya Haddasa Cece-kuce, Ta Hadu Matuka Hoto: hausaa_fulanii
Asali: Instagram

Sai dai kuma babban abun da ya fi jan hankalin mutane shine kyawun surar da Allah ya yiwa wannan amarya, domin dai irinta ake yiwa lakabi da ‘cocacola shape’.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun taya mijin nata murnar cewa ya yi dacen samun mace daya tamkar da dubu a bangaren kirar jiki mai kyau.

Kalli bidiyoyinta a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

faari1 ta ce:

“Ina kaunarta Wallahi ❤️.”

officialsojaboy ya yi martani:

“Mashaa Allah .”

a.a_abdul ya ce:

“Ikon Allah!”

phadles

“Amarya mai yayi dai.”

bosschic_rb ta ce:

“Ta dai saka kaya Hajia Zainab .”

amrish_babadiya ya rubuta:

“Allah bashi ikon daukan Nauyin da ya daura mishi.”

iam_ydeen ya ce:

“Toh Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basu ikon sauken nauyin da ke kansu, musamman kai ango akwai aiki jaa a gabanka, Allah yayi maka jagora! Ni nayi nan ♂️♂️.”

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

Uwargida Sarautar Mata: Kyawawan Hotunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami Tare Da Matarsa, Fatima Malami

A wani labarin, sabbin hotunan Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da uwargidarsa, Hajiya Fatima Malami sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.

A cikin hotunan, an gano Malami tare da iyalin nasa cikin ado inda suka fito shar da su.

Ministan ya sanya dakakkiyar farar shadda dinkin babbar riga da hula zannar bukar yayin da uwargidar tasa ke sanye da hadaddiyar leshi da mayafi yayin da wuyanta da kunne ke dauke da dankareriyar sarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel