Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya

Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya

  • Abubuwan mamaki basa taba karewa kamar yadda aka gano dan achaba yana jan motar bas da igiya
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an nuno dan achaba yana jan motar bas mai cin mutum 18 a kan gadar sama
  • Wannan al'amari ya baiwa mutane mamaki matuka inda suka tofa albarkacin bakunansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagas - Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana bidiyon wani dan achaba yana jan motar bas mai cin mutane 18.

A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka daure motar bas din wacce ga dukkan alamu ta samu matsala ne a jikin babur din da igiya.

Dan Achaba da motar bas
Ana Shagali A Lagas: Bidiyon Dan Achaba Yana Jan Motar Bas Mai Cin Mutum 18 Da Igiya Hoto: instablog9ja
Asali: Instagram

Sai direban babur din ya dungi jan motar a kan titi wanda ke dauke da cunkoson ababen hawa.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

Babban abun da ya fi bayar da mamaki shine duk wannan abun ya faru ne a kan gadar sama kuma daga dan achaban har direban bas din basu damu da hatsarin da ke tattare da wannan abu da suka aikata ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda shafin instablog9ja ya wallafa a Instagram, lamarin ya faru ne a jihar Lagas amma ba a bayyana takamaiman wurin da ya wakana ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun bayyana albarkacin bakunansu kan lamarin

tripple_b_collections ta yi martani:

“A kan doguwar gada kai Lagas/Ibadan.”

officialladyijay ta ce:

“A Najeriya komai zai iya faruwa…Muna ta rayuwa ne saboda tunaninmu!.”

mrlilgaga ya ce:

“Lagas, garin mahaukata.”

kemiite ya ce:

“A lagas kawai.”

Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami

Kara karanta wannan

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

A wani labari na daban, wani matashi dan shekaru 19 mai wasan barkwanci a Lagas, Eyinatayo Iluyomade, ya tsinci kansa a kurkuku bayan ya yi wasan barkwanci mai tsada ta hanyar ajiye wasikar fashi da makami a wani bankin zamani da ke garin Ondo, jihar Ondo.

Yan sanda sun gurfanar da Iluyomade a gaban kotu kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, barazana da kuma tin abubuwan da za su iya kawo barazana ga tsaro, jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya ce tuni aka sanya kudaden a asusun bankunan kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) na makarantun da za su amfana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel