Uwargida Sarautar Mata: Kyawawan Hotunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami Tare Da Matarsa, Fatima Malami

Uwargida Sarautar Mata: Kyawawan Hotunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami Tare Da Matarsa, Fatima Malami

  • Ko shakka babu Allah ya mallakawa Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, kyawawan mata
  • Wasu sabbin hotunan Malami tare da iyalinsa, Hajiya Fatima Malami sun bayyana a soshiyal midiya inda suka hadu tamkar wasu sabbin aure
  • An gano ma'auratan biyu cikin shiga ta alfarma yayin da suke kallon junansu cike da so da kauna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Sabbin hotunan Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da uwargidarsa, Hajiya Fatima Malami sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.

A cikin hotunan, an gano Malami tare da iyalin nasa cikin ado inda suka fito shar da su.

Malami da uwargidarsa
Uwargida Sarautar Mata: Kyawawan Hotunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami Tare Da Matarsa, Fatima Malami Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Ministan ya sanya dakakkiyar farar shadda dinkin babbar riga da hula zannar bukar yayin da uwargidar tasa ke sanye da hadaddiyar leshi da mayafi yayin da wuyanta da kunne ke dauke da dankareriyar sarka.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

A daya daga cikin hotunan, an nuno ma’auratan biyu suna kallon junansu cike da shauki yayin da fuskokinsu ke dauke da murmushin kauna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'a sun yi martani

5h_fabrics_abuja ta yi martani:

"Wow irin wannan walwali haka."

sherifatenigbokan ta sa:

"."

bilmaid ta ce:

"Mata nawa yake da shi."

syzeeeeeee ta yi martani:

"❤️❤️❤️❤️❤️❤️"

Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo

A wani labarin kuma, Kyakkyawar diyar tsohon zababben gwamnan jihar Zamfara, Mukhthar Idris Koguna mai suna Islam ta shiga daga ciki.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano zukekiyar amaryar cikin wata hadaddiyar doguwar riga irin na amaren zamani, kanta lullube da mayafi wanda aka jerawa duwatsu.

Abun birgewa kuma shine mahaifin nata da kansa ne ya daura mata wani dankararren sarkan wuya mai kyau domin cika adonta.

Kara karanta wannan

Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije

Asali: Legit.ng

Online view pixel