Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a Ondo

Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a Ondo

  • Wasu tsageru a jihar Ondo sun aikata mummunan barna, sun hallaka mai gadin gidan mai a jihar Ondo
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da bincike don dinke gano tsagerun
  • Ya zuwa yanzu, rundunar ta bayyana cewa, an kai gawar mai gadin dakin ajiye gawarwaki kafin daga bisani a yi jana'iza

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ondo - An kashe wani mai gadi mai suna Sunday a gidan man Titolu Venture da ke Igoba a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.

Mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin 4 ga watan Yuli, rahoton jaridar Daily Trust.

Tsageru sun kone gidan mai a Ondo
Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a Ondo | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Maharan da suka kai harin sun far wa gidan man ne kana suka fece. An ce an daure marigayin mai gadin ne kafin a harbe shi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Manajan gidan man, Ajisafe Oluwatobiloba, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin ne da misalin karfe 4 na safe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Da misalin karfe 4 na safe, daya daga cikin mazauna garin ya kira ni, da isata, sai muka ga gidan man na ci; mun kira hukumar kashe gobara suka zo kashe gobarar, ba tare da sanin wadanda suka aikata laifin sun kashe jami’in tsaron mu ba.
“A yayin da ake kokarin gano abin da ka iya haddasa gobarar, mun ga inda aka daure mai gadin aka kashe shi. Haka kuma mun ga kwalbar da tsagerun suka yi amfani da ita cike da man fetur wanda da ita aka yi amfani wajen ta da wutar.”

A halin da ake ciki, jami’an tsaro na ‘yan sandan Ondo da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru sun ajiye gawar mai gadin a dakin ajiyar gawa na asibiti, rahoton Tribune Online.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC na a wata jiha kurmus

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Misis Funmi Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano lamarin.

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

A wani labarin, a yau ne aka tashi da labarin kone wani ofishin hukumar zabe mai zaman kansa a wani yankin jihar Enugu, lamarin da ya girgiza 'yan Najeriya da dama, rahoton Daily Trust.

Kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana irin barnar da tsagerun suka aikata a ofishin na INEC a ranar Litinin a Abuja.

A cewar Okoye, Kwamishinan Zabe na Jihar Enugu, Mista Emeka Ononamadu, ya sanar da hedkwatar INEC cewa, a yayin harin, an lalata akwatunan zabe 748 da shingen kada kuri’a 240.

Kara karanta wannan

Hukuncin namijin da yaci amanar matarsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel