Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

  • Rahoton da ke iso mu ya bayyana cewa, akalla mutane shida ne aka hallaka a wani harin bindiga a kasar Amutka
  • Wannan ya faru ne a yau Litinin yayin da ake faretin bikin 'yancin kai na 4 ga watan Yulin wannan shekara
  • A kwanan nan Amurka na fama da yawaitar kisan gilla daga 'yan bindiga dadi da ke harbin kai mai uwa da wabi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Illinois , Amurka - Wani dan bindiga ya bude wuta a yau Litinin a wani faretin bikin ranar ‘yancin kai na Amurka a jihar Illinois, inda ya kashe akalla mutane shida, inji BBC.

Harin na dan bindiga harbin da aka kai a birnin Highland Park da ke kusa da Chicago, ya kuma yi sanadiyyar jikkatar mutane 24, kamar yadda 'yan sanda da magajin garin suka bayyana.

Kara karanta wannan

Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Amurka
Da dumi-dumi: An kashe mutane 6 a faretin ranar ‘yancin kai na Amurka | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Kwamandan ‘yan sandan Highland Park Chris O’Neill, kwamandan da ke kula da inda lamarin ya faru, ya bukaci jama’a da su fake yayin da hukumomi ke neman wanda ake zargi da aikata laifin, AlJazeera ta ruwaito.

Kakakin rundunar manyan laifuka ta yankin Lake Christopher Covelli ya bayyana a taron manema labarai cewa da alama dan bindigar ya bude wuta kan masu faretin ne daga saman wani rufi ta hanyar amfani da bindigar maharbin nesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidu sun bayyana ganin gawarwaki hade da jini da aka lullube da barguna.

Harbin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke kokarin dakile yawaitar tashe-tashen hankula da ake fama da su a kasar.

A baya-bayan nan an samu wasu munanan tashe-tashen hankula da suka hada da kisan kiyashi da aka yi a wata makarantar firamare ta jihar Texas, wanda ya cece-kuce da kira ga daukar tsaurara ka'idojin mallakar bindiga.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Dan shekara biyu ya bindige mahaifinsa har lahira yayin wasa da bindiga a Amurka

A wani labarin, wani yaro dan shekara biyu ya harbe mahaifinsa har lahira a Amurka yayin wasa da bindigar da iyayensa suka ajiye, hukumomi a birnin Florida ta Amurka suka bayyana ranar Litnin.

Yayinda jami'an yan sanda suka dira gidan ranar 26 ga Mayu, sun ga mahaifiyar yaron, Marie Ayala, na kokarin farfado da mijinta, Reggie Mabry, rahoton AFP.

Da farko jami'an tsaro sun dauka mahaifin ne ya harbe kansa amma daya daga cikin yaran gidan ya bayyanawa mahukunta cewa kaninsu dan shekara biyu ne yayi harbin, Shugaban hukumar yan sandan yankin John Mina ya bayyana haka a hira da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel