Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana barnar da wasu tsageru suka yi a jihar Enugu ta kudu maso gabas
  • Bayanin na zuwa ne awanni kadan bayan da wasu 'yan ta'adda suka bankawa ofishin INEC a wani yankin jihar wuta
  • Rahoton da muka samu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da kirga asarar da hukumar ta yi bayan tashin wutar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A yau ne aka tashi da labarin kone wani ofishin hukumar zabe mai zaman kansa a wani yankin jihar Enugu, lamarin da ya girgiza 'yan Najeriya da dama, rahoton Daily Trust.

Kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana irin barnar da tsagerun suka aikata a ofishin na INEC a ranar Litinin a Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Abubuwan da 'yan ta'adda suka lalata a ofishin INEC a Enugu
Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar Okoye, Kwamishinan Zabe na Jihar Enugu, Mista Emeka Ononamadu, ya sanar da hedkwatar INEC cewa, a yayin harin, an lalata akwatunan zabe 748 da shingen kada kuri’a 240.

Hakazalika, ya ce an lalata kayayyakin ofis da sauran kayayyakin aiki masu muhimmanci, duk da kokarin da hukumar kashe gobara ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Okoye:

“Hukumar na aiki don gano matsayin na’urorin rajistar masu kada kuri’a na (CVR) da ake yi da kuma katinan zabe na dindindin (PVCs) wadanda aka tattara a akwatin da wuta ba ta ci."

Matakin da ake dauka

Ya kuma ce an kai rahoto ga hukumar ‘yan sandan Najeriya domin gudanar da bincike da kuma daukar mataki.

Ya ce harin da ya zo a tsakiyar aikin rajistar katin zabe da sauran shirye-shiryen zaben 2023, abin damuwa ne, haka nan Punch a baya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC na a wata jiha kurmus

Hakazalika, ya tuna da yadda tsagerun a shekarar da ta gabata suka aikata mummunar barnar kone wasu ofisoshin hukumar ta INEC.

Ya zuwa yanzu, Okoye ya ce ana ci gaba da bincike tare da bin matakan da za su kai ga kammala ayyukan zabe a yankunan jihar nan da 2023.

Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC a yankin Enugu

A wani labarin, wasu tsageru sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.

Ofishin da ke hedikwatar majalisar a Ogurute ya kone kurmus a daren Lahadi kuma ginin da abin ya shafa ya kone gaba dayansa.

An tattaro cewa hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin shawo kan lamarin saboda fargabar harin da ka iya biyo baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel