Da Duminsa: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC a yankin Enugu

Da Duminsa: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC a yankin Enugu

  • Wasu tsagerun da ba a san ko su waye ba sun farmaki ofishin INEC a jihar Enugu ta kudu maso Gabashin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya da hukumomin zabe ke shirin zaben 2023 mai zuwa
  • Ya zuwa yanzu, an ce ofishin da ke wata karamar hukuma ya kone kurmus, kuma tabbas an yi asarar kayayyaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Enugu - Wasu tsageru sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.

Ofishin da ke hedikwatar majalisar a Ogurute ya kone kurmus a daren Lahadi kuma ginin da abin ya shafa ya kone gaba dayansa.

Yadda tsageru suka kone ofishin INEC a Enugu
Da Duminsa: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC a yankin Enugu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An tattaro cewa hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin shawo kan lamarin saboda fargabar harin da ka iya biyo baya.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Majiyoyi a yankin sun shaida wa The Nation cewa a lokacin da aka samar da tsaro a wurin, gobarar ta kone ginin gaba daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta kara da cewa, abin da motocin kashe gobara biyu daga Nsukka da Ogurute suka iya yi shi ne hana gobarar bazuwa zuwa ofisoshin da ke kusa.

Harin baya-bayan nan

A baya-bayan nan ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa Igboeze North da makwabciyarta karamar hukumar Igboeze ta Kudu hari, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe.

Hakazalika, gwamnati ta kuma haramta wa masu tuka babura a kananan hukumomin da abin ya shafa zirga-zirga, inji Independent.

Tun bayan barkewar rikici a yankin sama da wata guda da ya gabata, ana samun tsauraran matakan tsaro a yankin domin dakile yadda ake ci gaba da kai hare-hare yankunan jihar.

Kara karanta wannan

INEC ta bayyana damuwarta akan karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

A wani labarin, Gabanin zaben 2023, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni 2022 da Juma’a 1 ga Yuli 2022 a matsayin ranakun hutu a fadin jihar domin baiwa al’ummar jihar Neja damar mallakar katin zabe na PVC, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ya sanya wa hannu a ranar Alhamis a Minna.

Ya ce hutun, an ba da shi ne don baiwa ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman gwamnati da kuma ‘yan jihar da suka kai shekaru 18 damar karbar katunansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel