Kwararru: El-Rufai zai dauki malamai 10,000 aiki bayan ya kori sama da 2,000

Kwararru: El-Rufai zai dauki malamai 10,000 aiki bayan ya kori sama da 2,000

  • Gwamnatin Gwamna El Rufa'i ta ce za ta dauki malamai akalla 10,000 aiki a ma'aikatan ilimi ta jihar
  • Daukar aikin zai maye gurbin malaman da aka sallama kwanan nan kuma zai taimaka wajen bunkasa alakar malamai da dalibai
  • A halin da ake ciki, gwamnatin Kaduna ta sha alwashin ci gaba da yin waje da malaman da ba su cancanta ba a makarantun gwamnati

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kammala shirin daukar malaman firamare 10,000 domin maye gurbin wadanda aka kora domin inganta alakar malamai da dalibai, Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakiyar gwamnan, Dakta Hadiza Balarabe ce ta bayyana haka a Kaduna, a jiya, a wajen kaddamar da rabon kayayyakin koyo ga dalibai a makarantun firamare na gwamnati 4,260 da kuma cibiyoyin koyo 838.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Za a dauki malamai 10000 a Kaduna
Kwararru: El-Rufai zai dauki malamai 10,000 aiki bayan ta kori sama da 2,000 | Hoto: africanstudies.ox.ac.uk
Asali: UGC

A ranar 19 ga watan Yuni ne gwamnatin jihar ta sanar da korar malaman makarantun firamare 2,357 saboda rashin cin jarabawar cancanta da gwamnati ta yi musu, lamarin da ya jawi cece-kuce daga kungiyar malamai, inji Vanguard.

A shekarar 2018 ne gwamnatin jihar ta kori ma'aikata 21,780, saboda sun fadi irin jarabawar, yayin da kori wasu 233 a watan Disambar 2021 bisa zargin gabatar da takardu na bogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakiyar gwamnan ta ce gwamnati za ta ci gaba da korar malaman da ba su cancanta ba a makarantun gwamnati kuma babu wani abin damuwa da zai hana hakan.

A kalamanta:

“Ingantacciyar koyarwa tana da matukar muhimmanci wajen tantance sakamakon ilimi na yaranmu kuma ba za mu kyale ’ya’ya kalilan su sace ribar ba da da ilimi ba.
“Haka kuma ba za mu ci gaba da barin ilimi mara inganci ya kasance ga ’ya’yan marasa karfi ba a cikin al’ummarmu ba, wadanda ke zuwa makarantun gwamnati.

Kara karanta wannan

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

“Yaran talakawa suma sun cancanci kwararrun malamai, kuma alhakinmu ne da muka rantse mu tabbatar sun samu.”

Balarabe ta ce gwamnatin jihar ta gyara makarantun firamare da sakandare na gwamnati sama da 500 tare da samar da shingen makarantu da dama kamar yadda hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka bukata domin kula da yara.

Ta ce idan yaran talakawa suka fara samun litattafai da wuri, za su koyi karatu da kyau, ta kara da cewa idan yara suna samun litattafai za su iya koyon karatu cikin sauki.

Ta kuma bayyana cewa, za a rarraba kayan koyon karatun ne a karkashin shirin BESDA.

Korar Malaman Makaranta da El-Rufa'i ya yi a Kaduna ya saɓa wa doka, NUT

A wani labarin, shugaban ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya yi Allah waɗai da matakin korar malamai 2,357 a Kaduna bayan faɗuwa jarabawar cancanta.

Jaridar Vanguard ruwaito cewa Ɗalhatu ya ayyana matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka da ya saɓa wa doka.

Kara karanta wannan

Mun Kori Malamai 2,357 Ne Don Habbaka llimi, In Ji Gwamnatin Jihar Kaduna

A wata sanarwa da hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) ta fitar ta hannun Hauwa Muhammed, ta ce hukumar ta gudanar da jarabawa kan Malamai sama da 30,000 a watan Disamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel