Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

  • Gwamnan jihar Zamfara ya kaddamar da kwamiti 4 kan lamurran da suka shafi tsaro tare da samar da sabbin motoci 20 kirar Hilux da babura 1,500 don fara daukar matakai
  • Kafa kwamiti 4 wani bangare ne na aiki ba tare da gajiyawa da mulkinsa yake don shawo kan ta'addanci da ya dauki tsawon lokaci yana addabar jihar
  • Haka zalika, ya kara da cewa babu laifi idan mutum ya tsare kansa, sannan Nigeria Firearms Acts zasu horar gami da koya amfani da bindigogi ga duk wanda ke da ra'ayi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kaddamar da kwamitin tsaro guda 4 gami da samar da motoci 20 kirar Hilux da babura 1,500 don fara daukar matakai.

Sakataran watsa labaran gwamnan, Jamilu Iliyasu Magaji ne ya bayyana hakan ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Kwamitin sune kwamiti na musamman don tattara bayanan sirrin ta'addanci, kwamitin kula da tsaron anguwa (CPG), kwamitin gurfanar da masu laifukan da suka shafi ta'addanci, da kwamitin tabbatar da tsaron jihar.

Gwaman Bello Matawalle na jihar Zamfara
Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Matawalle ya ce kafa kwamitin wani bangare ne na kokarin da mulkinsa ke yi ba tare da gajiyawa don shawo kan annobar matsalar rashin tsaro da ta dauki tsawon lokaci tana addabar jihar da sauran jihohin yankin arewa-maso- yamma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bayyana yadda gwamnatinsa ta samar da duk wasu mafita masu bullewa don yi wa ta'addanci da sauran laifukan da suka shafi hakan garanbawul a fadin jihar.

Wadannan mafitar, a cewarsa, sun hada da tattaunawa, sulhu da dabarar aje makamai, yawan hada kai da gwamnatin tarayya a lamurran da suka shafi tsaro, hada kai da jihohin da ke makwabtaka da hukumomin Jamhuriyar Niger, datse kafar sadarwa don bawa jami'an tsaro damar kai samame ga sansanonin 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

"Muna sane da cewa yadda mutane da dama suka kalubalanci sabbin matakan da muka dauka, musamman yanke shawarar karfafa anguwannin da suke fama kusan kullum da zaluncin 'yan bindiga da su mallaki bindigogi don kare anguwannin su," a cewar Matawalle.
Ya ce kare kai abu ne mai kyau, kuma a koda yaushe wata dabara ce ta rayuwar bil'adama, inda yake cewa, "kamar yadda wasu suka yi amanna da tsare rayuka da dukiyoyin jama'a, za mu yi duk abun da zamu iya don tabbatar mun sauke wannan nauyin cikin dokokin shari'a."
Ya kara da cewa, "haka zalika, muna sane da yadda jami'an tsaro suke iya kokarinsu don magance wannan kalubalen. Sai dai, rashin isassun kayan aiki na zamani da karancin ma'aikata ne ya ke dakile kokarinsu.
"Matakin da muka dauka na shirya jama'a don tsare anguwanninsu, mun yi hakan ne don mutane su yaba da kokarin da jami'an tsaro keyi wajan yakar ta'addanci tare da zakulo masu ba wa 'yan ta'addan bayanai.

Kara karanta wannan

Zamfara: CDS Irabor ya Kalubalanci Umarnin Gwamna ga 'Yan Jihar na Mallakar Makamai

"Nigeria Firearms Acts sune zasu dauki nauyin koyawa da amfani da bindigogi ga duk wanda ke da ra'ayin yin haka."

A cikin makwannin nan, ya bayyana yadda jihar ta fuskanci hauhawar hare-hare a wasu yankunan Gusau, Bukkuyum da yankunan karamar hukumar Gummi, sannan jihar na taya mutanen kauyukan da lamarin ya shafa jaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel