Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

  • Hedkwatar tsaro ta bayyana yadda ranar Laraba dakarun OPSH tare da hadin guiwar mafarauta suka sheke 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar Filato da Kaduna
  • Haka zalika, dakarun sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa dasu a dajin kauyen Fanock na jihar Kaduna
  • Har ila yau, dakurun sun kama a kalla wasu 10 da ake zargin'yan fashi da makami ne a garin Kafanchan na karamar hukumar Jema'a cikin jihar Kaduna

Hedkwatar tsaro, a ranar Laraba ta ce rundunar Operation Safe Haven tare da hadin guiwar mafarauta, sun sheke 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a jihar Fulato da Kaduna.

An gano yadda 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka rasa rayukansu yayin wani samame na musamman da aka shirya a Fulato da jihar Kaduna, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Borno: Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji

Dakarun Sojin Najeriya
Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: Twitter

Wata takarda da daraktan ayyukan tsaro, Manjo-janar Benard Onyeuko ya fitar, ya bayyana yadda aka gano bindigogi kirar AK-47 biyu, carbin harsasai 101 mai girman 7.62mm, babur guda daya, mahakin karfe daya da bakaken rigunan sanyi biyu da sauransu yayin samamen.

Takarda ta bayyana yadda, "Rundunar Operation Safe Haven yayin kokarin da ta ke wajen kawo karshen hatsabibai a yankin da ta gabatar da aikin a ranar 28 ga watan Yuni, 2022 ta hanyar amfani da bayanan sirri, ta shirya kai samame tare da hadin guiwar 'yan sa kai a kauyen Kan Duniya na karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Fulato, inda suka sheke gagararrun 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Har ila yau a wannan ranar, dakarun sun fito samame inda suka yi ido biyu da wasu biyu da suke zargin masu garkuwa da mutane ne wuraren Sara High Ground cikin karamar hukumar Mangu ta jihar Fulato kan babur. Wadanda ake zargin sun yi fatali da babur din yayin da suka yi tozali da rundunar gami da ranta a na kare."

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Haka zalika, Onyeuko ya kara da bayyana yadda dakarun suka ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa dasu a dajen kauyen Fanock cikin jihar Kaduna.

A cewarsa, "Haka zalika, dakurun sun shirya tawagar bincike a kauyen Fanock na karamar hukumar Jema'a cikin jihar Kaduna inda suka gano wata mota kirar Toyota Corolla mai lamba ABUJA KUJ 452 AZ ba tare da kowa a ciki ba. Dakarun suka shirya bincike a dajin da ke zagaye inda suka ceto mutane uku mata biyu da namiji daya."

Onyeuko ya kara da cewa dakarun sun kama a kalla wasu da ake zargin 'yan fashi ne guda 10 a garin Kafanchan na karamar hukumar Jema'a cikin jihar Kaduna.

"Bugu da kari, a wannan ranar dakurun sun kama wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne guda 10 a garin Kafanchan na karamar hukumar Jema'a cikin jihar Kaduna.
"Wadanda aka kama sun hada da Messrs Manga Isma'il mai shekaru 22, Sani Bali mai shekaru 19, Idris Haruna (Ban Sambo) mai shekaru 20, Shamsuddeen Ladan mai shekaru 25, Abdulmajid Yau (Sele) mai shekaru 22, Abubakar Hassan mai shekaru 23, Abbas Aliyu mai shekaru 15, Muhammad Umar (Jazuli) mai shekaru 17, Jonathan Vincent (Bamai) mai shekaru 19 da Stephen Joseph mai shekaru 25.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

"Abubuwan da aka gano daga hatsabiban sun hada da: TV, DVD, Gas din girki, katifu, sifika, wayoyi, almakasai da sauransu. A halin yanzu ana cigaba da tuhumar su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel