Korar Malaman Makaranta da El-Rufa'i ya yi a Kaduna ya saɓa wa doka, NUT

Korar Malaman Makaranta da El-Rufa'i ya yi a Kaduna ya saɓa wa doka, NUT

  • Ƙungiyar Malaman Makarantu NUT reshen Ƙaduna ta yi Alla-wadai da matakin sallamar Malamai 2,357 bayan sun faɗi jarabawar gwaji
  • Shugaban NUT reshen Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya ce jarabawar gwajin da korar Malaman sun saɓa wa doka
  • Ya ce tun farko sun hana Malamai zama zana jarabawar bayan samun umarnin Kotu, amma tsoro ya sa suka rubuta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Shugaban ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya yi Allah waɗai da matakin korar malamai 2,357 a Kaduna bayan faɗuwa jarabawar cancanta.

Jaridar Vanguard ruwaito cewa Ɗalhatu ya ayyana matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka da ya saɓa wa doka.

A wata sanarwa da hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) ta fitar ta hannun Hauwa Muhammed, ta ce hukumar ta gudanar da jarabawa kan Malamai sama da 30,000 a watan Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna Ta Kori Malamai 2,357 Daga Aiki Ciki Har Da Shugaban Kungiyar Malamai NUT

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Korar Malaman Makaranta da El-Rufa'i ya yi a Kaduna ya saɓa wa doka, NUT Hoto: The Governor of Kaduna state/facebook
Asali: Facebook

Ta ce hukumar ta kori Malaman makarantun Firamare 2,192 ciki har da shugaban ƙungiyar NUT ta ƙasa bisa ƙin zama jarabawar gwaji da gwamnati ta gudanar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, Malamai 165 cikin 27, 662 da suka zauna jarabawar gwajin an kore su saboda gaza cin jarabawan.

Wani sashin sanarwan ta ce:

"Biyo bayan matsayar gwamnati na cigaba da gwajin Malamai domin inganta karatu ga yan Kaduna, KADSUBEB ta sake gudanar da jarabawar gwaji a Disamba, 2021. Ba'a buƙatar aikin Malaman da suka ci ƙasa da kashi 40, an sallame su."
"Malaman da suka ci kashi 75% zuwa sama ne suka tsallake gwajin kuma sun cancanci su halarci horarwa kan shugabanci da harkokin koyarwa a makarantu. Malaman da suka ci tsakanin kaso 40-75% za'a sake basu dama don inganta kwarewar su."
"Muna tabbatar wa malamai da sauran al'umma cewa zamu cigaba da yin duk abin da zai kawo cigaba da inganta ilimin kananan yara da sauran ɗalibai."

Kara karanta wannan

2023: 'Ka ci amanar mu' Gwamna Okowa da Atiku ya zaɓa mataimaki ya shiga tsaka mai wuya

Martanin NUT

Da yake martani shugaban NUT, Ibrahim Dalhatu, ya bayyana jarabawan gwajin da kuma korar malamai da cewa sun saɓa wa doka.

Guardian ta ruwaito shugaban NUT na cewa:

"Mun sami umarnin Kotu na hana hukumar gudanar da gwajin, ta yi kunnen uwar shegu da umarnin doka. Mun umarci Malamai ka da su zauna jarabawan saboda mun gano wata maƙarƙashiya ce da aka shirya don korar su."
"Mun gargaɗi Malamai cewa duk wanda ya zauna jarabawan wacce ta saɓa doka ba zamu kare shi ba, amma wasu suka banzatar da mu suka rubuta saboda tsoro."
"Bamu ƙi a gudanar da gwajin ba amma abi matakai da ya dace, bai kamata a yi amfani da ita wajen korar ma'aikata ba. Kamata ya yi a yi jarabawan da nufin gano inda malamai ke da rauni, a shirya horarwa don ƙara musu kwarewa."

A wani labarin kuma mun haɗa muku wasu Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

Ɗan takarar jam'iyyar All Progressive Congress APC, Mista Biodun Oyebanji, ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ekiti wanda ya gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022.

Da yake ayyana wanda ya samu nasara, baturen zaɓe na hukumar INEC , Farfesa Oyebode Adebowale, ya ce Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 da suka ba shi damar zama zakara a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel