Mun Kori Malamai 2,357 Ne Don Habbaka llimi, In Ji Gwamnatin Jihar Kaduna

Mun Kori Malamai 2,357 Ne Don Habbaka llimi, In Ji Gwamnatin Jihar Kaduna

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi magana game da korar malaman makarantun frimare su 2,357 da ta yi a jihar a kwana-kwanan nan
  • Tijani Abdullahi, Shugaban hukumar Shugaban hukumar ilimi bai daya na Jihar Kaduna, KADSUBEB ya ce an dauki matakin ne don inganta ilimi
  • Abdullahi ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba jihar za ta dauki sabbin malamai guda 10,000 don tabbatar da daidaita tsakanin adadin malamai da dalibai

Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna, a jiya ta yi martani kan korar malaman frimare guda 2,257 daga jihar, The Nation ta rahoto.

Gwamnatin Jihar, a cikin makonni da suka gabata, ta kori fiye da malamai 2,000 ne makarantun firamare saboda rashin kokari da cancanta.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

Taswirar Jihar Kaduna.
Gwamnatin Kaduna: Mun Kori Malamai 2,357 Ne Don Habbaka llimi. @MobilePunch.
Asali: UGC

Ta kuma kori shugaban kungiyar malamai, NUT, na Jihar Kaduna saboda rashin rubuta jarrabawar sanin makamashin aiki da ta wajabtawa malamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban hukumar ilimi bai daya na Jihar Kaduna, KADSUBEB, Tijani Abdullahi, a jiya ya ce korar malaman kan abin da ake kira rashin kokari/cancanta an yi ne don inganta ilimin frimare a jihar.

Gwamnatin Kaduna za ta dauki sabbin malamai 10,000

Ya ce jihar ta kori malamai fiye da 2,000 saboda tana son samun ingantaccen ilimi da kuma habbaka ayyukan NUT.

A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamnati kan lamarin, shugaban na SUBEB ya ce ana shirin daukan sabbin malamai 10,000 don samar da daidaito tsakanin yawan malamai da dalibai.

Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban alkalan Najeriya Tanko Muhammad

A wani rahoton, kungiyar kwadago na kasa reshen jihar Kaduna ta alakanta rashin tsaro a jihar da korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta ce gwamnatin Nasiru El-Rufai ta kori ma'aikata 30,000 tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2015.

Babban sakataren kungiyar hadaka ta AUPCTRE, Comrade Sikiru Waheed, shi ne ya bayyana haka yayin bikin ranar ma'aikata a Abuja.

AUPCTRE, reshen kungiyar gwadago ta kasa, ta ce za ta goyi bayan kungiyar kwadago kan makomar ma'aikatan a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel