Zamfara: Za A Fara Rataye Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane

Zamfara: Za A Fara Rataye Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane

  • Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya rattaba hannu kan dokar zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga yan bindiga da masu garkuwa
  • A karkashin sabuwar dokar da majalisar dokokin Jihar Zamfara ta yi, an tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa, barayin shanu, yan bindiga, masu yi musu leken asiri da sauransu
  • Matawalle ya ce dokar da za ta fara aiki nan take za ta bawa gwamnatin damar hukunta duk wanda aka samu da laifin a karkashin doka da nufin magance kallubalen tsaro a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle, a ranar Talata, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta yaki da yan bindiga da laifuka masu alaka a jihar, rahoton Daily Nigerian.

A karkashin dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk dan bindiga da laifuka masa alaka da hakan a Zamfara.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan bindiga sun sace shanu yayin da suka kai hari wurin kiwonsu kusa da filin jirgi

Gwamna Bello Matawalle.
Za A Fara Rataye Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane a Zamfara. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar, Matawalle ya ce dokar na cikin matakai ne na yaki da yan bindiga, masu garkuwa da satar shanu a Zamfara.

Majalisar Dokokin Jihar ta Zamfara ta amince da kudirin dokar ne a ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2022.

Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa a karkashin doka don kare mutanen jiharsa.

"Za mu cigaba da bibiyan hanyoyin samar da tsaro a Zamfara a karkashin mulki na.
"Ya kamata wadanda ke sukar matakan da na dauka don samar da tsaro su yi la'akari da halin da muke ciki na hare-haren yan bindiga.
"Su duba mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da aka kashe wa, raunatawa da garkuwa da su a kullum a sassa daban na jihar," in ji shi.

Kara karanta wannan

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

Gwamnan ya ce jami'an tsaro masu kare unguwanni ba su da banbanci da dakarun JTF na Borno da Amotekun a kudu maso yamma.

Ya ce sabuwar dokar za ta bada daman hukunta wadanda aka samu da hannu wurin hare-haren yan bindiga da laifuka masu kama da su a karkashin doka.

"Duk wanda aka samu da laifin harin yan bindiga, garkuwa, satar shanu, kungiyar asiri ko yi wa yan bindiga leken asiri zai fuskanci hukuncin kisa," ya kara.

Ta kuma bada damar yanke hukuncin daurin rai da rai, daurin shekaru 20 ko 10 ba tare da zabin biyan tara ba ga wanda aka samu yana taimakawa masu aikata laifi.

Matawalle ya yaba wa majalisar jihar don jajircewa wurin yin aikinsu na doka.

Za a fara rataye masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga a Niger

A wani rahoton, majalisar dokokin jihar Niger ta yi sabuwar doka wacce ta bada umurnin a rika yanke wa duk wanda aka tabbatarwa laifin garkuwa da mutane ko dan bindiga hukuncin kisa ta hanyar rataya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

News Wire ta ruwaito cewa 'yan majalisar sun kuma ce dokar za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu yana hada baki ko taimakawa yan bindiga da masu garkuwa a jihar.

Majalisar dokokin jihar yayin zamanta na ranar Talata ta amince da kudin yi wa dokar hana garkuwa da mutane da satar shanu ta shekarar 2021 kwaskwarima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel