Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

  • Motar tanka dauke da man fetur makil ta yi bindiga a kan babban titin Lokoja zuwa Abuja a cikin jihar Kogi
  • An gano cewa, rayuka uku sun salwanta sakamakon mummunan hatsari da gudun direban motar ya haddasa
  • Motar kaya dake ajiye a gefen titin tare da wasu ababen hawa har biyu duk sun kurmushe sakamakon hatsarin

Lokoja, Kogi - A kalla rayukan mutum uku ne suka salwanta a daren Litinin yayin da tanka dauke da mai ta yi bindiga a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Lamarin, kamar yadda rahotanni suka nuna, ya faru ne mintoci kadan kafin karfe 8 wurin Felele kan babban titin Lokoja zuwa Abuja yayin da birkin motar ya kwace.

Tankar mai
Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja. Hoto daga chaannelstv.com
Asali: UGC

Tankar tana kokarin sauka daga tudun titin wanda sakamakon hakan ne birkin ya kwace, tankar ta fadawa wata motar kaya dake gefen titi, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

A wani yunkurin da direban yayi na tsayar da motar, tsananin karfin bugun yasa tankar ta kama da wuta inda ta bar gawawwaki uku har ba a iya gane su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lamarin ya bar matafiya masu yawa da masu ababen hawa babu hanyar wucewa.

Kwamandan bangaren na hukumar kiyaye hadurra a titunan tarayya, Stephen Dawulung, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata a Lokoja.

Ya kara da cewa, an ceto mutum biyu bayan sun samu muguwar kuna kuma aka kai su Cibiyar Lafiya ta Tarayya dake babban birnin jihar domin samun taimako yayin da aka mika gawawwakin ma'adanar gawa.

"Hatsarin ya faru ne sakamakon tukin gangancin da direban yake yi wanda hakan yasa motar ta kubce masa," cewar Dawuling.
"Direban tankar ya kone kurmus. Motar kaya dake ajiye a gefe da wasu ababen hawa biyu duk wutar ta shafe su."

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Takardar haihuwar matashin da zai bayar da koda ya nuna shekarunsa 21 ba 15 ba – Hukumar NIS

Kamar yadda yace, jami'an FRSC da aka tura wurin sun kawai gyara cunkoson dake titin bayan ibtila'in ya yi sauki.

Jami'in FRSC din ya ja kunne direbobi, ballantana wadanda ke dauke da abubuwa masu iya kamawa da wuta da su dinga kiyayewa tare da tuki a sannu.

Ya jaddada bukatar dukkan ababen hawa su kiyaye dokokin kariya na ababen hawa domin gujewa zubewa abinda suke dauke da shi a yayin da hatsari ya auku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel