Za a fara rataye masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga a Niger

Za a fara rataye masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga a Niger

  • Majalisar dokokin jihar Niger ta yi dokar da za ta bawa kotu damar yanke wa masu garkuwa da mutane da yan bindiga hukuncin rataya
  • Majalisar jihar ta kuma ce dokar ta yi tanadin duk wanda aka samu yana taimakawa yan bindiga ko masu garkuwa shima hukuncin rataya zai hau kansa
  • Majalisar ta ce ta yi wannan dokar ne da nufin kawo karshen hare-haren da yan bindiga da masu garkuwa ke yawan kaiwa a jihar

Majalisar dokokin jihar Niger ta yi sabuwar doka wacce ta bada umurnin a rika yanke wa duk wanda aka tabbatarwa laifin garkuwa da mutane ko dan bindiga hukuncin kisa ta hanyar rataya, Daily Trust ta ruwaito.

News Wire ta ruwaito cewa 'yan majalisar sun kuma ce dokar za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu yana hada baki ko taimakawa yan bindiga da masu garkuwa a jihar.

Taswirar jihar Niger.
Taswirar jihar Niger. Hoto: The Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

Majalisar dokokin jihar yayin zamanta na ranar Talata ta amince da kudin yi wa dokar hana garkuwa da mutane da satar shanu ta shekarar 2021 kwaskwarima.

Kungiyoyin bata gari sun kasance suna kai hare-hare a sassan jihar har ma da makarantu inda babu cikakken tsaro sannan su sace dalibai su tafi da su daji domin neman a biya su kudin fansa.

KU KARANTA: Kungiyar ACTED da Zulum ya dakatar a Borno ta bayyana dalilin da yasa ta ke bawa ma'aikatanta horaswa

Idan za a iya tunawa, a watan Mayun wannan shekarar yan bindigan sun afka garin Tegine a jihar Niger inda suka sace dalibai a wata makarantar Islamiyya.

Mafarauta sun ɗirkawa mai garkuwa harsashi ya mutu wurin karɓar kuɗin fansa

A wani rahoton daban, mafarauta sun harbe wani mutum da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane uku har lahira yayin da ya tafi karbar kudin fansa a kauyen Abobo a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mafarauci da ke cikin wadanda suka shirya atisayen, ya ce an yi harbin ne misalin karfe 5.23 na asubahi a ranar Talata.

Mutumin ya fito ne daga wurin da ya ke boye a yankin Abobo, bayan Itakpe, wasu yan kilomita kadan daga babban titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel